Fasinjojin AZMAN sun yi zanga-zanga kan soke tafiya a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ɗaruruwan fasinjojin jirgin Azman ne a safiyar ranar Talata da ta gabata suka mamaye hedikwatar kamfanin domin nuna rashin amincewarsu da soke jirginsu.

Da farko an shirya jirgin Kano zuwa Legas da ƙarfe 7:30 na safe. Manhaja ta kalato cewa fasinjojin da suka yi zanga-zangar sun koka da rashin jin daɗin sokewar da aka yi musu ba zato ba tsammani, inda suka nuna rashin amincewarsu da lamarin saboda babu wata sanarwa kafin ɗaukar matakin.

Fasinjoji biyu, mata da miji da za su bi jirgin a kan hanyarsu ta zuwa Landan sun nuna takaicinsu kan abun da ya faru.

Shi ma wani fasinja wanda zai bi jirgin akan hanyar sa ta zuwa Sudan, domin neman magani ya bayyana yadda soke jirgin ya haifar masa da matsala, inda ya bayyana cewa zai sanya ya rasa jirgin da zai ɗauke shi a ranar.

Wani ɗan majalisar dokokin jihar Kano wanda shi ma yana cikin jirgin da a ka soke ya ce hakan ya janyo masa cikas kan taro mai muhimmanci da ya yi niyyar halarta a Legas.

Babban jami’in tsaro na kamfanin jirgin Bashir Otaru wanda ya yi jawabi ga fasinjojin ya bayyana takaicinsa kan lamarin.

Ya ce, an soke tashin jirgin ne saboda wata matsala da jirgin ya samu. Ya ce, za a shiryawa fasinjojin wani jirgi a yammacin Laraba, yayin da waɗanda ke so a dawo mu su da kuɗinsu za dawo mu su da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *