Everton ta kori Rafael Benitez kwanaki 200 bayan ba shi aikin horarwa

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton ta kori Manajanta Rafael Benitez kwanaki 200 cif bayan ba shi aikin horarwa daidai lokacin da ƙungiyar ke ci gaba da fuskantar tarin rashin nasara a wasanninta na Firimiya.

Benitez wanda ya yi aiki tsawon lokaci da Liverpool da ke matsayin babbar abokiyar dabin Everton ya karɓi ragamar ƙungiyar ne a watan Yunin 2021.

Sanarwar da ƙungiyar ta wallafa a shafinta ta tabbatar da raba gari da kocin nata bayan shan kaye a wasanni 9 cikin wasanni 13 da ƙungiyar ta doka a baya-bayan nan ƙarƙashin gasar firimiyar Ingila.

Rashin nasara ta baya-bayan nan da Everton ta yi shi ne shan kayenta a hannun Norwich asabar ɗin nan da ƙwallaye 2 da 1.

Duk da cewa ƙungiyar ba ta sanar da wanda zai maye gurbin Benitez ba, amma wasu bayanai na ganin zai yi wuya idan Wayne Rooney bai karɓi ragamar ƙungiyar ba, ko da ya ke Frank Lampard da Chelsea ta raba gari da shi a bara wanda kuma dama tsohon ɗan wasan ƙungiyar ne.

Zuwa yanzu Everton na matsayin ta 16 ne da maki 19 bayan doka wasanni 19 ƙarƙashin gasar Firimiyar Ingila wanda ke nuna duk manajan da zai karɓi aikin horarwa zai ci karo da babban ƙalubale.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *