Cire tallafin mai: Gwamnoni sun yi wa Tinubu mubaya’a

Daga BASHIR ISAH

Gwamnoni 36 a faɗin ƙasa, sun bayyana goyon bayansu ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu dangane da batun cire taffin mai.

Gwamnonin sun bayyana haka ne yayin ganawar da Shugaban Ƙasar ya yi da Ƙungiyar Gwamnoni (NGF), ranar Laraba a fadarsa da ke a Abuja.

Gwamnonin ƙarƙashin jagorancin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, sun bayyana farin ciki da gamsuwarsu game da matakin cire tallafin mai da Shugaba Bola ya ɗauka.

Kazalika, sun bai wa Tinubun tabbaci tare da ɗaukar masa alƙawarin za su yi aiki tare a kan haka.

Tun farko da yake jawabi, Shugaba Tinubu ya yi kira ga gwamnonin da su haɗa kai da Gwamnatin Tarayya wajen yaƙi da talauci a faɗin ƙasa.

Shugaban ya kuma buƙaci shugabannin siyasa da su ajiye bambance-bambancen da ke tsakani sannan a dunƙule wuri guda don kawar wa jama’ar ƙasa wahalhalun da suke fuskanta.

A cewarsa, “Muna iya ganin tasirin talaucin da jama’a ke fama da shi a fuskokinsu. Talauci ba gadonsa ake yi ba, matsala ce daga al’umma.

“Matsayinmu shi ne mu kawar da talaucin. Mu ajiye bambancin siyasa a gefe, mun zo ne domin tattaunawa game da Nijeriya da kuma gina ƙasa,” in ji Tinubu.

Ya ƙara da cewa al’ummar Nijeriya tamkar ‘yan gida ɗaya ne, kuma shugabanci nagari shi ne zai taimaka wajen inganta harkar dimokuraɗiyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *