Daga BASHIR ISAH
Fitaccen ɗan siyasar jihar Anambra kuma tsohon ɗan Majalisar Tarayya, Sanata Annie Okonkwo ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 63 a duniya.
Rasuwar tasa na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki kaɗan kafin rantsar da ɗansa, Hon. Uche Harris Okonkwo, a matsayin mamba a Majalisar Wakilai ta ƙasa.
A halin rayuwarsa, Okonkwo ya yi sanata mai wakiltar Anambra ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.
Majiyarmu ta ce marigayin har ya soma murmurewa daga rashin lafiyar da yake fama da shi bayan samun kulawa a wani asibitin Amurka.
Amma daga bisani jikin nasa ya sake rikicewa inda a ranar Laraba ya ce ga garinku nan.
Majiyar ta ƙara da cewa, nan ba da jimawa ba za a fitar da tsare-tsaren binne mamacin da zarar ahalinsa sun haɗu sun tattauna.
Marigayin ɗan asalin ƙauyen Ojoto ne cikin Ƙaramar Hukumar Idemili ta Kudu, Jihar Anambra. Kuma a halin rayuwarsa, ya yi karatu da sauran harkoki a gida da wajen Nijeriya.