Csaba Korosi: Sin ta zmo babbar garkuwa ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MƊD

Daga CMG HAUSA

Shugaban babban taron MƊD na 77 Csaba Korosi ya bayyana cewa, ƙasar Sin a matsayin babbar garkuwa ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MƊD.

Mr. Korosi, wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin taron taya murnar cika shekaru 73 da kafuwar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin, wanda ofishin wakilcin Sin a MƊD ya kira ta kafar bidiyo.

Ya ce a matsayinta na daya daga cikin ƙasashen da suka assasa MƊD, kuma wakiliyar dindindin a kwamitin tsaron majalissar, Sin ta taka rawar gani yadda ya kamata.

Korosi ya kuma taya Sin murnar manyan nasarorin da ta cimma a fannin ingiza ci gaba da wadatuwar al’ummarta.

Ya ce “Manufar ƙasar Sin ta ciyar da duniya gaba, na ƙunshe da damar ingiza samun ci gaba mai ɗorewa, da aiwatar da ajandar ci gaba ta MƊD ta nan da shekarar 2030”.

Taron da ofishin wakilcin na Sin a MƊD ya kira, ya samu mahalarta kusan mutane 200, da suka haɗa da manyan jami’an MƊD, da wakilan dindindin na ƙasashe daban daban, da manyan jami’an diflomasiyya daga sama da ƙasashe 100, da ’yan jarida daga kafofin watsa labarai na kasa da ƙasa da dama, da kuma aminan ƙasar Sin daga fannonin rayuwa daban daban.

Mai Fassarawa: Saminu Alhassan