‘Yan bindiga sun kashe sufeton ‘yan sanda, sun sace fasinjoji a kan hanyar Katsina zuwa Jibiya

Daga UMAR GARBA a Katsina

‘Yan bindiga da ke aikin ta’addanci a dajin Ƙaramar Hukumar Jibiya dake cikin Jihar Katsina sun kashe wani sufeton ‘yan sanda mai suna Idris Musa a unguwar Maƙera da ke yankin Kwakware a kan hanyar Katsina zuwa Jibiya.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar Katsina SP Gambo Isa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewar iftila’in ya rutsa da jami’in ɗan sandar a lokacin da yake tafiya cikin motarsa zai nufi wurin aiki.

Wani da lamarin ya faru a gaban idonsa muka kuma sakaya sunansa ya shaidawa Manhaja cewar ‘yan bindigar sun isa unguwar ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 7:00 na safe suna harbe-harbe a lokacin da suke bin wata motar safa da ke ɗauke da wasu fasinjoji.

Ya cigaba da cewa sufeton ‘yan sandan ya yi yunƙurin fatattakar ‘yan ta’addar sai dai sun yi galaba a kansa, inda suka buɗe masa wuta bayan sun kashe shi suka kuma ƙone masa mota.

Daga nan sai ‘yan bindigar suka yi awon gaba da wasu fasinjoji dake kan hanyar waɗanda kawo yanzu ba a tantance yawan su ba.

Daga ƙarshe kakakin rundunar ya bayyana cewar ana cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *