Da Ɗumi-Ɗumi: Alƙali ya umarci a yi waje da Nnamdi Kanu ana tsaka da shari’a

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Alhamis Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya ya umurci jami’an tsaro su yi waje da tsararren jagoran ƙungiyar ƴan fafatukar kafa ƙasar Biafara (IPOB) Nnamdi Kanu daga farfajiyar kotu yayin da ake tsaka da shari’a.

Hakan na zuwa ne yayin da Kanu ya yi ta ƙoƙarin tada hayaniya yayin da ake sauraren ƙara da aka shigar akansa.

Jagoran na IPOB ya buƙaci alƙalin ya njna masa inda doka ta haramta masa shigar da rubutaccen adireshi, lamarin da ya sa Omotosho ya dakatar da shari’ar da umartar jami’an tsaro su yi waje da shi.

Da fari kotun ta yi watsi da sabon ƙorafin da Kanu ya yi a gabanta, inda ta ce sun ƙunshi ababen da aka riga da warware su a zama da aka yi a baya.

Haka kuma, Alƙalin ya ƙi amince wa buƙatar Kanu ta miƙa shari’ar tasa ga Kotun Ɗaukaka Ƙara, inda ya bada hujjar haramcin hakan a ƙarƙashin kundin manyan laifuka sashe na 306.

Rikicin ya faro ne a lokacin da Mai Shari’a Omotosho ya yi yunƙurin karanta shari’ar, inda Kanu ya tirje akan kotun ba ta da ikon ƙin yin la’akari da rubutaccen adireshinsa, lamarin da ya janyo cece-kuce da fitar da shi a kotun.

By Babaji