Shugaban Kasa Bola Tinubu ya nada jamrumi a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu, a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Harkoki Fina-finai ta Nijeriya.
Kazalika, nadin ya shafi wasu mutum 10 wadanda za su jagoranci sassa daban karkashin Ma’aikatar Fasaha, Raya Al’adu da Karfafa Tattalin Arziki.
Bayanin nadin na kunshe ne cikin sanarwar da ta fito ta hannun Kakakin Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale, a ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, Tinubu ya bukaci wadanda nadin ya shafa su aiki da kwarewa don cigaban kasa.
Wadanda nadin ya shafa sun hada da:
(1) Tola Akerele — Director-General, National Theatre
(2) Dr. Shaibu Husseini — Director-General, National Films and Censors Board
(3) Mr. Obi Asika — Director-General, National Council for Arts and Culture
(4) Aisha Adamu Augie — Director-General, Centre for Black and African Arts and Culture
(5) Ekpolador-Ebi Koinyan — Chief Conservator, National War Museum
(6) Ahmed Sodangi — Director-General, National Gallery of Art
(7) Chaliya Shagaya — Director-General, National Institute of Archeology and Museums Studies
(8) Hajiya Khaltume Bulama Gana — Artistic Director, National Troupe of Nigeria
(9) Otunba Biodun Ajiboye — Director-General, National Institute for Cultural Orientation
(10) Ali Nuhu — Managing-Director, Nigerian Film Corporation (11) Ramatu Abonbo Mohammed — Director-General, National Commission for Museums and M
