DA ƊUMI-ƊUMI: ‘Yar ƙunar baƙin wake ta halaka mutum shida da bom a Borno

Spread the love

Wata da ake zargin yar ƙunar bakin wake ce, ta tashi bam a mararaban Gwoza da ke jihar Barno. Wanda hakan yayi sanadiyar aƙalla mutane shida da jikkata wasu da dama.

Wadda tai ƙunar bakin waken, ance mace ce wadda bata wuce shekara 20 ba. Bayanan sirri sun tabbatar mafi yawan wanda abun ya rutsa dasu, farar hula ne. Kuma sun dawo ne daga wani biki.

Ma’aikatan asibiti sun tabbatar da mutuwar mutum shida da kuma jikkatar mutum 15. Kwamishinan ‘ƴan sandan jihar Barno Yusuf Lawal ya tabbatar da faruwar wannan al’amari.

By ukarofi