DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Kano ta umarci ƴan sanda su fitar da Aminu Ado daga gidan sarki na Nassarawa don ta yi kwaskwarima

Daga Ibrahim Hamisu

Gwamnatin jihar Kano ta umurci kwamishinan ‘yan sanda da ya fitar da Sarkin Kano na 15, Aminu Bayero daga gidan sarki na Nasarawa GRA da ke yake zaune.

A yayin wani taron manema labarai da kwamishinan shari’a na jihar Kano Barista Haruna Isa Dederi ya yi, ya bayyana cewa gwamnati ta kammala shirye-shiryen sake gina gidan Sarkin.Gwamnatin ta kuma bada umarnin sake gina katangar gidan saboda ta lalace.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da a yammacin yau babbar Kotun tarayya dake Kano Karkashin jagorancin mai shari’a Abdullahi Liman ta yanke hukuncin rushe duk wani mataki da gwamnatin Kano ta dauka game da sabuwar dokar Masarautu wacce Majalisar dokokin jihar Kano ta yiwa gyaran fuska.