Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad Elrufai, ya ce da ya ga dama sai ya saka jami’an tsaro su kama ɗan takarar Shugabancin Ƙasa a ƙarƙashin inuwar LP, Peter Obi.
El-Rufa’i, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron zuba jari na Kaduna karo na 7.0, wato Kadinvest da ya gudana ranar Asabar a Kaduna.
Gwamnan na Kaduna ya ce wani lokaci a baya da ya kai ziyarar bibiyar lamuran zave a jihar Anambra, sai da Peter Obi ya sa aka tsare shi awanni 48, saboda shine gwamna a jihar.
Ya ce da yana so sai ya yi ramuwar gayya tunda Peter Obi, shi ma zai zo yawon siyasar sa a jihar Kaduna, tunda shi ne Gmamna kuma yana da iko da jami’an tsaro, inda ya bayyana cewa yana da bataliyar sojoji na NDA da sauran barikin jami’an tsaro a cikin Kaduna.
Sai El-Rufa’i ya yi masa gugar zanar cewa, ba zai kama shi ba, saboda ‘yan Arewa “muna da dattako da kuma wayewa.”