Likitocin asibitin ATBU sun duba lafiyar direbobi 180 a Yankari Express

Daga MU’AZU HARDAWA a Bauchi

A ƙoƙarin su na tallafa wa direbobi da ma’aikatan kamfanin sufuri na Yankari Express, da ke Bauchi, ƙwararrun likitoci kan harkar ido sun duba mutane 180 a ƙarƙashin shirin bikin ranar gani ta duniya wato World Sight Day na Majalisar Ɗinkin Duniya wanda ke kasancewa a ranar kowace Alhamis ta biyu a cikin watan Oktoba, inda a bana ya kasance ranar 13 ga Oktoba.

Likitoci daga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi sun duba lafiyar idon direbobin kamfanin sufara na Yankari Express inda suka ba mutane 90 tabarau da magani wa sauran waɗanda aka duba.

Bayan haka kuma za a yi wa mutane tara aikin ido kyauta a asibitin Amsad da ke Bauchi.

Dr. Shahir Bello Umar na ɗaya daga cikin manyan likitoci da suka jagoranci aikin, ya ce sun gudanar da aikin cikin nasara. Bayan haka sun yi aikin ne don su taimaki direbobin saboda akwai wanda sun jima suna tuƙa mota amma saboda sana’ar su ce ta cin abinci ba su daina ba, kuma ba su tashi tsaye sun magance matsalar ba, alhali hakan na iya jawo hatsari maimakon a ɗauki matakin kariya tun da wuri lamarin na iya kaiwa ga raunata mutane ko rasa rayuwa.

Don haka ya ce ya zamo wajiba mutane idan sun kai shekaru 50 su riƙa zuwa ana duba lafiyar su ta auna ciwon suga da hawan jini da lafiyar idon su don samun kariya daga makancewa ko kamuwa da cututtukan zamani.

Dr Funmilayo Oyediji ta kasance cikin tawagar likitoci da suka gudanar da aikin inda ta bayyana wa wakilin mu cewa rigakafi ya fi magani, don haka ya zamo wajibi kowa ya san muhimmancin idonsa ya kiyaye shi saboda rashin ido mutuwar tsaye ce da koma baya ga rayuwa.

Wasu daga cikin direbobi da aka duba sun yaba game da taimakon kamar yadda Malam Yakubu Shehu direba ya ce an duba shi an ba shi magani kuma za a masa aiki saboda akwai yana ta sauko a kan idonsa don haka ya gode da wannan taimako musamman a wannan lokaci da ake fama da matsalar abin da za a kai bakin salati.

Shi ma Malam Habu Musa ya ce ya ji daɗin duba idon sa da aka yi kuma an ba shi tabarau don yin karatu saboda yadda yake samun matsala idan yana karatu bayan haka ya ƙara da cewa akwai matarsa ita ma na fama da matsalar ido kuma sun ba shi shawara ya kai ta asibiti don a duba a gano abin da ke damun idon ta saboda rigakafi ya fi magani.