Dalilan da ya sa yan sanda ba za su fitar da Sarki Aminu Ado ba- Kwamishinan ‘yan sanda

Kwamisshinan Yan sandan Jihar kano, AIG Usaini Gumel ya bayar da dalilan da ya sa ba su bi umarnin Gwamnan Kano ba na tsige Aminu Ado Bayero daga gidan sarki da ke Nasarawa.

In bamu manta ba, Gwamnan kanon ta hannun Kwamishinan sharia na jihar kano, Bar Haruna Isa Dederi ya fitar da sanarwar wadda ta umarci Kwamishinan ya tsige tsohon sarkin da gidan.

Sai dai Kwamishinan ‘yan sandan a wata hira da aka yi dashi ta wayar salula ya ce bin umarnin gwamnatin zai kasance gaggawa ne, saboda gwamnatin da ta bayar da wannan umarnin ta kuma shigar da ƙara kotu a kan lamarin. Ya ƙara da cewa tunda lamarin yana kotu dole sai sun jira su ga mai kotu za ta ce.