Dalilin da ya sa muka bada umarnin tsare Doyin Okupe – EFCC

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta ce, ta bayar da umarnin tsare tsohon mai ba Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan shawara kan Harkokin Jama’a, Doyin Okupe, bisa buqatar sa-ido da ta gabatar a ranar 18 ga watan Yulin shekarar 2016, sama da shekaru shida kafin a yanke masa hukunci a kan tuhume-tuhumen kuɗi da babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi.

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama tsohon Shugaban Ƙungiyar Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP, Doyin Okupe.

A cewar lauyansa Tolu Babaleye, an kama ɗan siyasar ne a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Ikeja a Jihar Legas, a lokacin da ya ke shirin tafiya Landan.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, ta samu Okupe, mai bai wa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan shawara kan Harkokin Jama’a, da laifin karkatar da kuɗaɗen makamai daga Ofishin tsohon mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro.

Mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta bayyana cewa, masu tuhuma sun gabatar da ƙarar satar kuɗi a kan Okupe wanda aka ci shi tarar Naira miliyan 13.

A shekarar 2019, Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziki Zangon Ƙasa (EFCC), ta tuhumi Okupe da laifuka 59 ciki har da waɗanda suka shafi karkatar da kuɗi har Naira miliyan 240 daga hannun Sambo Dasuki.

An gurfanar da shi tare da wasu kamfanoni biyu, Value Trust Investment Ltd da Abrahams Telecoms Ltd.

Mai shari’a Ojukwu, ta samu Okupe da laifuka 26 daga cikin tuhume-tuhume 59 da EFCC ta gabatar a kansa.

Alƙalin ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu kan kowanne laifi daga cikin tuhume-tuhumen 26 ko kuma zaɓin biyan tarar N500,000 a kan kowanne laifin.

Alqalin ta kuma bayar da umarnin cewa idan ba a biya tarar cikin sa’o’i 24 ba, za a tisa ƙeyar Okupe zuwa gidan yari, lamarin da ya yi gaggawar cika wa’adin saboda gudun zaman wakafi.

A cewar Babaleye, DSS ta bukaci Okupe ya gabatar da hanyoyin da ya bi wajen biyan tarar kuɗaɗen da kotun ta yanka masa.

Har yanzu dai hukumar DSS ba ta ce komai kan ikirarin lauyan nasa ba.

Okupe dai ya ajiye muqaminsa na shugabancin yaƙin neman zaɓen Peter Obi bayan da aka yanke masa hukunci, inda hadimin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, Akin Osuntokun ya maye gurbinsa.

A wani labari kuma, Hukumar EFCC ta saki Doyin Okupe sa’o’i bayan kama shi a filin jirgin saman Legas.

A baya an ruwaito cewa jami’an tsaro na farin kaya (DSS) sun kama Okupe a filin jirgin sama na Muritala Mohammed, Legas da safiyar Alhamis, 12 ga watan Janairu, 2023.

By Editor