An shiga watan taƙaitawa da daina aiki da tsoffin kuɗi

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

An shiga watan taƙaitawa da kuma daina aiki da tsoffin kuɗi. Wannan ya ƙara bayyana ne bayan isa 9 ga watan nan na Janairu inda ya ke ƙa’idar taƙaita fitar da kuɗi a na’urorin kuɗi na ATM a Nijeriya. Babban bankin Nijeriya CBN ya fara aiwatar da sabuwar ƙa’idar da kuma nuna hakan ba zai kawo wata matsala ba a Nijeriya.

Tuni hakan na nuna an fara aiki da tsarin nan na rage amfani da takardun kuɗi don haka ya zama ko dai kowa ya yi ƙoƙarin komawa aiki da na’urori ko kuma ya riƙa shan ɗawainiya kan hada-hada da kuɗi. Duk da haka su kan su masu aiki da na’urar za su yi fama da taƙaita adadin kuɗin da za sui ya fitarwa a wuni da kuma mako. Matakai biyu ne babban bankin ya kawo a lokaci ɗaya da duk su ka samu suka daga akasarin ’yan ƙasa ciki kuma har da ’yan majalisa da ke zaman wakilan jama’are kowane sashe a tarayya.

Daga farko kan batun taqaita fitar da kuɗi ’yan majalisa sun ba da shawarar ƙara yawan kuɗin don dacewa da buƙatun al’umma tun da in an duba fitar da Naira dubu 20 a wuni ga ɗaiɗaiku da dubu 100 ga kamfanoni ba zai samu karɓuwa ba. ’Yan majalisar sun ce sun samu kira daga jama’a daga mazaɓarsu cewa lalle a sauya tsarin don ba zai haifar da alheri ba. Matsa lamba wataƙila ya sa babban bankin ƙara yawan kuɗin duk da nan ma ba wani kari da mutane musamman ’yan kasuwa ke farin ciki da shi ba ne. In manyan ’yan kasuwa masu hulɗarsu a birane na iya taɓukawa da sabon tsarin, tuni ƙananan ’yan kasuwa a ƙauyuka ke nuna tsarin zai kawo mu su babbar illa.

Akwai labaran da ke nuna wasu ma ba sa yarda sam a ce za a biya su ta hannun wasu da amfani da na’urar nan ta POS. Gaskiya a na samun ƙarancin matakan wayar da kan jama’a da kuma rashin la’akari da bambancin jama’ar wajen tsare-tsare ko aiwatar da wasu muhimman shirye-shiryen gwamnati. Bayanaai na nuna wasu ƙasashe ba sa taƙaita fitar da kuɗi sai dai akwai caji a fitarwa ko shigar da kuɗin kamar yadda ya ke a Nijeriya. Kazalika ƙasashe kan canja kuɗi amma hakan ba ya saka su daina amfani da duk takardun kuɗin da su ke yawo a kasuwa.

Tsarin shi ne a hankali a tsawon shekaru za a riƙa janye tsoffin kuɗin a hankali har su kare. Ko da wani zai voye kuɗi bayan an ɓullo da sabbi, to duk ranar da ya fito da kuɗin sa zai kashe ba tare da wata fargaba ba. Hikimar sauya kuɗi a irin waɗannan ƙasashen shi ne don ƙara matakan kariya ga kuɗin da kuma wataƙila sanya sabbin hotunan mutane bayan shuɗewar shugabannin da hotunan su ke kan kuɗin. Rashin bin irin wannan tsari ya kawo zargi ma a canja kuɗin inda wasu ke fargabar ko ma dabara ce ta hana ’yan hamayya samun wadatattun kuɗin da za su ɗauki nauyin kamfen da lamuran zaɓe.

A nasa bayanan da su ka ɗan saɓa da wannan gwamnan Adamawa Umaru Fintiri kamar yadda a ka ruwaito shi a kamfen ya na cewa gwamnan babban bankin tamkar ya na hamayya da ’yan siyasa ne don kasa samun damar amfana daga takarar siyasa. In za a tuna an ga hotunan gwamnan bankin lokacin zaven fitar da gwanin jam’iyyar APC na nuna ya na neman tikitin takarar jam’iyyar don gadon shugaba Buhari. Rashin samun nasarar Emefiele ta zama a kan kujerar gwamnan banki ga kuma matsayin ɗan takarar jam’iyyar gwamnati ya jawo ya ke neman huce haushin sa kan ’yan siyasa.

A na cikin wannan muhawara sai a ka ga faifan bidiyo na tsohon gwamnan bankin Sarki Sunusi Lamido Sunusi ya na mai cewa taƙaita fitar da kuɗin ko komawa aiki da na’ura zai taimaka wajen hana ’yan siyasa masu zummar maguɗi yin hakan. Tsohon gwamnan ya ce shi ya kawo tsarin ma tun 2012 amma bai karaɗe ƙasa ba.

A cewar Lamido Sunusi hakan zai hana masu babakere damar amfani da kuɗi wajen sayen ƙuri’a don haka kenan an kange su daga bin varauniyar hanya wajen maƙalewa a madafun iko. A inda gizo ke saƙar kusan ’yan siyasa ƙalilan ta kowane ɓangare daga waɗanda a ke ganinsu na da gaskiya da akasin haka da ba sa amfani da kuɗi wajen samun goyon baya. Talauci ya yi tsanani a tsakanin talakawa a Nijeriya. Ma’ana in har mai sukuni zai iya kawar da kai daga karvar kyautar ɗan siyasa zai yi matuƙar wuya ga wanda ba shi da abincin wunin yau ba ya ƙi karɓar kuɗin.

Kai lamarin fa ya kai in za a ba da kuɗin har rantsar da mutum za a yi ya ɗauki alƙawarin ƙuri’arsa ga wanda ya miƙa kuɗin. Wata al’ada ma har wasu kansa a yi alwala a zo a rantse da Alƙur’ani kafin a miƙa irin waɗannan kuɗin. La’akari da mutane da su ka haɗa da talakawan talak kan buƙaci kuɗi don samun na abinci, masu kamfen da ke ganin ba sa ba da kuɗi kuma kamarsu na da magoya baya kan ce jama’a in an ba su kuɗi su karba amma kar su zaɓi waɗanda su ka ba da kuɗin.

Duk wannan ba ma matsaya ce mai kyau ba a ce mutum ya karɓi kuɗi amma ya ki cika alƙawari ga wanda ya ba shi kuɗin. Shawarar da ta fi dacewa ka da kowa ya yaudari kowa. Matuƙar mutum ya na da aƙidar zaɓar mutum ba don kuɗi ba to kar ya karɓi kuɗin, idan kuma ya karɓa kar ya ɗauki alƙawari ko amincewa da sharaɗin lalle zai zavi wanda ya ba da kuɗi. Ai shi ya sa ba a samun sauyi a wasu sassan don wasu masu zaɓen da ma ’yan takarar kan yi wa juna munafurci. Gaskiya da gaskiya kawai ta dace ga ’yan Nijeriya har dai a na son samun cigaba mai ma’ana.

Tsohon ɗan Majalisar Dattawa kuma masanin harokin kuɗi Sanata haruna Garba ya ce shawarar da Majalisar Dattawa ta ba wa babban bankin Nijeriya CBN na tsawaita lokacin canja kuɗi har zuwa ƙarshen watan Yuni shi ne daidai da yanayin Nijeriya don matsayar majalisa tamkar doka ce ga sassan gwamnati in an duba haƙƙin majalisar ne tsara dokoki.

Sanata Garba na sharhi ne kan matakan babban bankin Nijeriya na sabunta kuɗi da kuma taqaita adadin kuɗi da za a iya cira daga asusun bankuna da su ka zo kusan a lokaci ɗaya. Tsohon ɗan Majalisar Dattawan ya ce ya na da muhimmanci babban bankin ya mutunta matsayar Majalisar Dattawa kan wannan tsari da ya shafi rayuwar ’yan ƙasa baki ɗaya.

Dalilan da babban bankin ya bayar na dawo da kuɗi banki don yadda mutane su ka riƙe fiye da Naira tirilyan 2.7 cikin tiriliyan 3.2 da a a buga; a ra’ayin Garba hujja ce da za ta sake tsananta matakin a dan ƙanƙanin lokaci ba don an samu lokaci da kuɗin su ka koma hannun jama’a a gida da ba ya rasa nasaba da rashin tabbas na bankuna.

Hakanan ya ce, nazarin sabunta kuɗin zai kawo ƙarshen satar mutane ba ma tunani ne mai ma’ana ba don tabbas ya rage ga wanda ƙaddara ta sa a ka sace ɗan uwan sa ya san yadda zai nemo kuɗi don ceto ɗan uwan na sa. Don haka a nazarin Haruna Garba ɓarayin mutane ba za su daina ba don an canja kuɗi ko an taƙaita fitar da kuɗi a wuni.

A tabaron Sanata Garba, tsarin ya na da kyau amma sai an samu wadataccen lokacin aiwatar da shi sannan ne za a cimma nasara.

Gwamnan babban banki Godwin Emefiele ya bayyana cewa tsoffin kudin za su cigaba da aiki zuwa 31 ga watan nan na Janairu amma daga nan sai sabbin kuɗin kaɗai.

Fargabar rashin wadatar sabbin kuɗin da zuwa yanzu alƙaluman bankin na nuna an buga kimanin Naira miliyan 500 ne na ƙaruwa kuma wa’adin dakatar da tsoffin kuɗin na ƙaratowa.

Ɗan majalisa Gudaji Kazaure da ke cigaba da aikin binciken cajin shigarwa da fitar da kuɗi a banki, ya ce illar da canjin zai kawo ba zai misaltu ba.

Wasu bankuna sun tura saƙon cewa za a iya samun sabbin kuɗin a na’urorin ATM a faɗin ƙasar da fitar da Naira dubu 100 ga ɗaiɗaiku dubu 500 ga kamfanoni.

Kammalawa;

Yanzu dai za a jira a ga yadda babban bankin zai saurari shawarar majalisa ta tsawaita daina amfani da tsoffin kuɗin zuwa watan Yuni ko kuwa a’a. A dai lokacin da na ke wannan rubutu ba alama ta zahiri ta ƙara wa’adin bayan isa 31 ga watan nan.

Fiye da mutum ɗaya a matsayin gwamnan banki, ya na da kyau duk sauran daraktocin bankin su riƙa duba hagu da dama kan sabbin manufofi da su ke kawowa da ma gaiyato wasu ƙwararru daga wajen bankin don ba da shawara. Sauraron irin tunanin talakawa ma ya na da kyau don duk mai mulki na cewa ya na yin aiki ne don inganta rayuwar talaka.