Don bambance wa duniya tsakanin Kudu da Arewacin Nijeriya na fara shirya fim ɗin Turanci – Jammaje

“Nan da shekaru 10 masu ilimi ne za su ƙwace Kannywood”

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Kabiru Musa Jammaje shahararren malamin koyar da Turanci a Nijeriya, Sannan ya kasance furodusa da yake shirya finafinai da Ingilishi a masana’atar Kannywood, a tattaunawar sa da wakilin Manhaja a Kano, Ibrahim Hamisu, za ku ji cikakken tarihinsa da nasarorinsa har ma da irin qalubalen da ya fuskanta a lokacin da ya fara yin fim ɗin Turanci a Masana’atar Kannywood. Ga dai yadda hirar ta kasance:

MANHAJA: Za mu so ka gabatar mana da kanka?

Jammaje: Sunana Kabiru Musa Jammaje, shugaban Makarantar Jammaje Acadamy, kuma mai shirya finafinai a masana’atar Kannywood a ƙarƙashin Kamfanin Jammaje Production.

Rayuwar karatu fa?

Na yi makarantar primary da secondary, bayan na kammala, na shiga makarantar Kass inda na karanci harshen Turanci, amma dai ban gama ba sai na sami admissions a BUK inda na ƙaranci English, daga nan sai na tafi Atlanta English Institute da ke Ƙasar Amurka. Kuma ni har yanzu ɗalibi ne a National Open University inda na ke karanta Educational Administration of Learning a matakin digree na biyu, wanda yanzu sauran kaɗan na kammala, da na gama zan ɗora da digiri na uku.

Da yawan mutanen Nijeriya sun sanka ne matsayin mai koyar da Turanci da buga littafai. Ta ya ka samu kanka a masana’atar fim ta Kannywood?

Da ma dai tun kafin na shiga Ina da abokai a masana’atar Kannywood. To wata rana na tafi Ƙasar Afirka ta Kudu a shekarar 2010 da kuma Kenya a 2011 muka yi mu’amala da su, na ce, masu ni ɗan Nijeriya ne, sai suka ce ai suna kallon finafinanmu, wato suna nufin Nigrian films waɗanda ake yi da Turanci, suna ganin yadda ake nuna maita da tsafi da sauransu, sai suka ce duk yadda akai muma matsafa ne kuma madanfara ne da sauransu.

Ni Kuma sai na ce masu waɗannan finafinai a na yin su ne a Kudancin Nijeriya, ni kuma daga Arewa na ke, kuma waɗannan abubuwan ba sa wakiltar mu, ba a’ladunmu ba ne, mu aladarmu daban, amma dai ba su yadda ba, suka ce ai ɗan Nijeriya kawai ɗan Nijeriya ne don haka su ba su yadda ba.

To wannan ne ya sa na fara tunanin yin finafinai da turanci domin su zagaya duniya yadda ake kallon waɗancan mu ma ya zama an kallemu, akwai finafinai da ake yi da Hausa to Ƙasar Hausa babban harshe ne, amma am fi yin amfani da shi a Afirka ta Yamma shi kuma English ana yin amfani da shi duk duniya, to idan ka yi fim da Hausa an fi yin amfani da shi a Afirka ta Yamma to amma idan ka yi da English duk duniya za ta iya kalla, wannan ne ya sa na ce ya kamata na fara yin finafinan Hausa da Turanci domin su shiga lungu da saqo na duniya a ga ɗabi’unmu da al’adunmu.

To dama akwai Falalu Dorayi wanda darakta ne, duk da yake yanzu ya zama jarumi, ɗalibinmu ne a lokacin a Jammaje Acadamy, na same shi muka tattauna inda na samu goyon baya daga Falalu Dorayi da Abba Almustapha, sai Iliyasu Umar Mai kuɗi ya rubuta labarin, aka ɗauki fim ɗin mu na farko, kuma alhamdu lillahi, ya yi nasara fiye da yadda aka zata.

Da wane fim ka fara kuma a wace shekarar ?

Na fara yin fim a shekarar 2016, kuma na fara da fim ɗin ‘This Is the way’.

Ya zuwa yanzu finafinai nawa ka fitar?

Ya zuwa yanzu na yi finafinai guda biyar, dukkaninsu da Ingilishi, waɗanda suka haxa da: ‘There is a way’ a 2016 sai ‘Lights and darkness’, sai ‘This is the way’, dukka a 2017, sai 2018 muka yi ‘In search of the’, kuma sai kuma 2019 muka yi ‘Nanjala’ wanda muka yi a Abuja inda muka haɗa da Jaruman Nollywood, shi bai fito ba tukuna da yake an kashe kuɗi da yawa a nan bin hanyoyi don mayar da kuɗi an kuma a ci riba.

To kwalliya ta biya kuɗin sabulu kuwa bayan ka fitar da fim ɗin farko a 2016?

Gaskiya ta biya, domin lokacin da ya zo kasuwa ana buga CD, manya manya finafinai da suka fito dukka ya ba su ruwa, an kalli shi sosai, bayan mun buga sai da muka sake bugawa, kuma da kuɗinsa ne muka buga ‘Light and Darkness’ wanda Rahama Sadau da Rabi’u Rikadawa suka taka muhimmiyar rawa a cikinsa.

A cikin shekara shida da ka fara yin fim zuwa yanzu waɗanne irin nasarori za ka iya cewa ka samu?

Gaskiya na samu nasarori guda biyu: nasara ta farko ta Kannywood ce gabaɗaya, domin da ana ganin ‘yan Kannywood ɗin ba su yi karatun boko ba, to zuwan Jammaje Production sai ya sa aka gane cewa da yawansu akwai waɗanda suka yi karatun boko, sannan na biyu shi ne, hankalin ‘yan Nollywood ya karkato ga Kannywood, suka ga cewa waɗannan da suke yin finafinai da Hausa yanzu ga shi suna yi da Turanci, to sai aka daɗa samun alaqa, sai ya zama zaka riƙa ganin Jaruman Nollywood suna zuwa Kannywood ana yin fim da su na Hausa da na Turanci, suma suna zuwa a na yi da su, duk da yake ana yi, amma zuwan mu ya qara wa abin tasiri da ƙarfi.

Sai ni a ƙashin-kaina, kamfanina ya samu karɓuwa a wajen al’umma, sannan makaranta da na kafa ta koyar da Turanci finafinan sun taimaka mata sosai, domin wata mata ta taɓa zuwa ta ce, Turanci da na ga ana yi a fim ɗinku ga yarana na kawo su a koya masu irin sa. Kuma ya zuwa yanzu duk wani babban gari a Arewacin Nijeriya za ka ga cewa mun buɗe reshe, yanzu haka muna da reshe 30 a Arewa. Kum da finafinan muke yin talla, ka ga wannan ma babbar nasara ce.

Ƙalubale fa akwai ko babu?

Eh akwai, ƙalubale shi ne yadda za ka ga cewa da yawan ‘yan Kannywood suna ganin mu munzo ne da niyyar ƙwace Kannywood ɗin, amma a hankali na kwantar masu da hanhaki cewa ni da su zan yi amfani, saboda haka da ‘yan masana’atar muka rinƙa yin amfani, muna yin aikace-aikacenmu tun daga kan ma’aikatan fim ɗin da kuma jaruman, amma daga baya sun lura cewa, abin cigaba ne ba abin tsoro ba ne. Duk da yake mun samu ‘yan matsaloli ta yadda idan muka kira jarumi zai mana ‘acting’, to sai ya amsa zai zo mun dogara da shi sai ya ƙi zuwa, wata kila yana ganin ko za a ƙure shi ko kuma Turancin nasa bai yi ƙarfin da zai iya fitowa a fim ba, wani sai a qarshe muke fuskantar ba zai zo ba, alhali ka dogara da shi, mun samu waɗannan matsaloli gaskiya.

Menene burinka a masana’atar fim ta Kannywood?

Burina shi ne, na ci gaba da samar da finafinan Tarihi da al’adun Arewa, domin idan ka duba finanan da muka yi na zamantakewa ne ‘In seach of the king’ shi ne za a iya cewa na al’ada, amma sauran duk na zamantakewa ne. Kuma yanzu haka Ina da labarai kwanan nan zan fito da su, kuma labarai ne da suke fito da gargajiya, tarihi da al’ada ta Malam Bahaushe, ka ga kuwa finafinai ne da duniya ta ke buƙatar su domin su kalla a harshen Turanci.

Ya ka ke kallon masana’atar Kannywood nan da shekara 10?

Gaskiya nan da shekara 10 na hango cewa waɗanda suka yi karatu suke da Ilimin fim su ne za su ƙwace ta, to ka ga duk wanda bai tsaya ya yi karatu ba, ba na jin yana da wuri a masana’atar.

Ya ka ke ganin yawaitar kwararowar masu son yin fim daga jahohi daban-dadan musamman mata?

Gaskiya ne hakan na faruwa, shawara da zan bayar a kai shi ne, a sa mataki na Ilimi, ta yadda za a ce sai ka na da mataki na ilimi kaza za ka fito a fim, to Ina ganin za a rage kwararowarsu, to idan akai haka za ka ga cewa, wanda ya shigo ɗin ya cancanta kenan, misali za a iya cewa ba za ka shigo masana’atar ba sai ka na da NCE ko Diploma, idan an ga shi ma ya yi yawa sai a ce sai ka na da Degree ko HND sanna za ka shiga. Ƙasar Indiya haka suke yi da za ka ga kowa na shiga barkatai, to daga baya suka sanya cewa sai ka na da Degree aƙalla sannan ka za ma jarumi, sai idan mutum ya gada ne to yana ciki sai ya ci gaba da yin karatun.

Menene shawarka ga su kansu shugabannin Kannywood?

Shawara ta ita ce, su shugabanni su samar da wancan tsarin na matakin ilimi kafin shigowa da na faɗa a baya, domin ko ni da ba na cikin shugabanni a na yawan yi min waya da magana ta Whastapp, akan ana son shigowa cikin Kannywood, kuma za ka ga cewa da yawansu ko karatun Hausa ba su iya ba, to ka ga mutum ko kaɗan bai yi makaranta ba kenan, amma yana so ya shiga masana’atar. Za ka iya cewa kusan a kan haka aka gina masana’atar, wato an bai wa waɗanda ba su yi karatu ba dama. Domin idan da anyi to yanzu lokaci ne da ya kamata a daina shigowa barkatai, wasu suna da ‘talent’ ba su da ilimi to kamata ya yi a haɗa talent da ilimi, sai ya zama idan ka zo kana son shiga, kuma da talent to sai ace ga matakin ilimi da ake buƙata wannan shi ne babban abin da ya kamata shuganni su yi.

Me za ka ce dangane da yawaitar fim mai dogon zango da ake ya yi yanzu, cigaba ko ci baya?

Ta wani ɓangaren cigaba ne ta wani ɓangaren kuma ci-baya ne, ci-baya ne ta yadda za ka ga kamar an daina fim mai gajejrin zango, wato feature Films, ita kuma duk wata masananta ta duniya ba ta taƙama da kawai Series, da feature fim ta ke taqama, domin su feature film idan masana’ata tana yin sa to ta zauna da ƙafafunta. Amma ko a Amurka idan ka na son duniya ta sanka to sai ka fara da fim mai dogon zango sai ya zama gada ce da za ta haɗa su da can din. Kuma su feature fim idan a na yin su masana’ata ta zauna da gindin ta kenan. Duk da yake ya taimaka wajen samar da sababbin jarumai da aikin yi. Amma bai taimaka mata a matsayinta na masana’anta ba.

Menene fatanka ga masoya da masu kallon finafinanka?

Abinda zance shi ne, sun ɗan ji ni shiru kwana biyu, to su yi hakuri, yanzu haka akwai finafinai guda uku zuwa huɗu da muka rubuta, labarai ne da sun fi na da, kuma Abubakar Maishadda da yake yanzu da shi muke aiki ya yi mana albishin na kayan aikin, wato kyamarori da duk kayan aiki idan mun tashi yin finafinanmu zai ba mu kayan aiki kyauta, ka ga alhamdu lillahi mun samu sauƙi, kuma kaya ne na zamani.

Madalla. Mun gode.

Ni ma na gode matuƙa.