EFCC ta fara binciken aikin samar da lantarki na Mambilla

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Majalisar Dattijai ta bayyana cewa, Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) tana gudanar da wani cikakken bincike kan aikin samar da wutar lantarki na Mambila da ya kai Dala biliyan shida.

Da ya ke magana a Abuja lokacin da ya bayyana a gaban Sanata Gabriel Suswan, ɗan jam’oiyyar PDP daga Jihar Benuwe a Arewa ta Tsakiya tare da kwamitin Majalisar Dattawa kan kare kasafin kuɗin 2023, Ministan Wutar Lantarki, Injiniya Abubakar Aliyu, ya ce, ma’aikatar ta gana da masu ruwa da tsaki kuma a halin yanzu ana ƙoƙarin warware dukkanin matsalolin.

Ya ƙara da cewa, batun shari’a kan aikin wutar lantarki na Mambilla na kawo cikas ga aikin.

Ministan wanda ya yi magana a lokacin da Sanata Gabriel Suswan ya nuna damuwa game da halin da ake ciki a aikin samar da wutar lantarki na Mambilla, ya ce, “game da Mambilla, mun gana da masu ruwa da tsaki kuma muna shawo kan lamarin. Akwai batun shari’a a ciki.

“EFCC ta shiga cikin lamarin kuma mun ba su bayanai game da lamarin, mun ba su tarihin aikin samar da wutar lantarki, lauyoyinmu sun yi mu’amala da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, idan har ba mu janye ƙarar, ba za mu iya ba komai ba.

“Ba na tsammanin masu saka hannun jari za su kawo kuɗinsu inda akwai matsala.”

Da ya ke magana kan aikin, kwamitin majalisar dattijai mai kula da wutar lantarki ya bayyana cewa aikin samar da wutar lantarki na Mambilla ya tsaya cak duk da tanadin kasafin kuɗin shekara na biliyoyin kuɗi.