FIFA U17: Flamingos ta kai mataki na kusa da ƙarshe

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Mata ta Nijeriya (Flamingos) ta samu nasarar tsallakewa zuwa mataki na kusa da ƙarshe na gasar Kofin Duniya na FIFA na mata ‘yan ƙasa da shekara 17 wanda ke gudana a Indiya.

Flamingos ta samu wannan nasara ne bayan da ta lallasa takawararta ta Amurka da ci 4-3 a bugun fenariti.

An buga wannan wasa ne a ranar Juma’a, 21 ga Oktoba, 2022.