Fitattun kisan da suka tada hankali a Arewa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ‘yan shekarun nan, ana yawan samun rahotannin kisan-gilla a Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya inda akasari kisan ke tayar da hankalin jama’a.

Duk da cewa a faɗin Nijeriya ana samun rahotannin kisan kai akai-akai, amma irin waɗanda ake samu a Kano na jan hankali saboda abubuwan da ke tattare da kisan musamman na ban al’ajabi ko tsananin tausayi ko kuma wani abu da hankali bai cika ɗauka ba.

Dangane da irin waɗannan abubuwa, Blueprint Manhaja ta yi nazari dangane da kisan-gilla biyar da suka yi matuƙar tayar da hankali a Kano.

Kisan Fatima Abubakar da ‘ya’yanta shida

A ranar Asabar, 17 ga Janairun 2026 ne aka samu rahoton kisan Fatima Abubakar mai shekara 35 a unguwar ɗorayi Charanchi da ke cikin birnin Kano tare da ‘ya’yanta shida.

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce ana zargin maharan da amfani da muggan makamai wurin aikata wannan ta’asar.

Bayan samun wannan rahoto, kafofin sada zumunta sun ɗauki ɗumi matuƙa inda ake ta alhinin faruwar wannan mummunan lamari da addu’ar kamo waɗanda ake zargi da aikata ta’asar da hukunta su.

Sai dai a safiyar Lahadi rundunar ‘yan sandan ta fitar da sanarwa inda take tabbatar da kama mutum uku waɗanda ake zargi da kisan.

A yayin samamen, ‘yan sandan sun gano tufafi masu ɗauke da jini, makamai, da kayayyakin da aka sace, yayin da bincike ke ci gaba.

Kisan Nafiu a Kano

Kisan da ake zargin wata matar aure mai suna Hafsat ta yi wa wani matashi a Jihar Kano mai suna Nafiu Hafiz a shekarar 2023 ya jawo ce-ce-ku-ce a lokacin da lamarin ya faru sakamakon yadda aka rinƙa samun bayanai daban-daban da suka rinƙa fitowa masu ɗaure kai.

Rahotanni sun nuna cewa wadda ake zargin wato Hafsat, da ita da mijinta iyayen gidan marigayin ne, kuma abin ya faru ne a gidansu da ke Unguwa Uku a Kano.

Labarin kisan Nafiu dai ya karaɗe shafukan sada zumunta a faɗin Nijeriya, kuma batun ya ɗauki hankali sosai inda ya jawo ce-ce-ku-ce da Allah wadai daga faɗin ƙasar.

Kisan Hanifa

Kisan Hanifa wadda yarinya ce mai shekara biyar a Kano ya yi matuƙar tayar da hankalin jama’a sakamakon yadda lamarin ya kasance mai ban tausayi da takaici.

Bayan kisan Hanifa, Babbar Kotun Kano ta yanke wa malaminta Abdulmalik Tanko hukuncin kisa bayan samunsa da laifin garkuwa da Hanifa da laifin kisanta da kuma laifin kitsa yadda za a yi garkuwa da ita.

Tun da farko malamin na su Hanifa ne ya haɗa kai da wasu domin sace ta inda daga baya ya kashe ta sannan ya binne ta a cikin wani buhu.

Sai dai tun bayan yanke wa Abdulmalik hukuncin kisa, babu wani ƙarin bayani game da aiwatar da hukuncin na kisa a kansa.

Ummita da ɗan China

A shekarar 2022 ne aka zargi wani ɗan ƙasar China mai suna Geng ƙuangron da kashe budurwarsa mai suna Ummulkulsum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita.

Shi ma wannan lamarin ya tayar da ƙura wanda hakan ya sa aka shafe makonni ana tafka muhawara a shafukan sada zumunta.

A lokacin da lamarin ya faru, an zargi ɗan ƙasar Chinan da bin Ummita har gidansu da ke unguwar Janbulo inda ya soka mata wuƙa wanda hakan ya yi ajalinta.

Daga baya an gurfanar da Mista Geng a gaban kotu inda ya amsa laifin kisan Ummita tare da cewa ya kashe mata kuɗi fiye da Naira miliyan 60.

Mahaifiyar da ta kashe ‘ya’yanta biyu a Kano

A watan Oktoban 2020 ne kuma aka shiga wani hali na ruɗu a birnin Kano, bayan da aka yi zargin wata uwa da kashe ‘ya’yanta har biyu a Unguwar Sagagi.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar yaran, Yusuf Ibrahim mai shekara biyar da ‘yar uwarsa Zahra’u Ibrahim mai shekara uku.

A shekarar 2020 ne wani lamari mai kama da almara wanda ya matuƙar jawo ce-ce-ku-ce ya faru a unguwar Sagagi a Kano bayan wata mata ta kashe ‘ya’yanta biyu.

Ana zargin matar da kashe ‘ya’yanta biyu waɗanda suka haɗa da Yusuf Ibrahim mai shekara biyar da Zahra’u Ibrahim mai shekara uku bayan mijin ya yi barazanar yi mata kishiya.

Sai dai a bayanin da iyayen matar suka yi wa ‘yan sanda, sun ce ‘yarsu na da taɓin hankali tsawon shekaru.

ƙona mutane a masallacin Gezawa

A ranar 15 ga watan Mayun 2024 aka wayi gari da wani mummunan iftila’i da za a jima ba a manta da shi ba a Kano, bayan da wani matashi ya cinna wa masu ibada wuta a cikin masallaci sannan ya kulle su a lokacin sallar asuba.

Lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 23, inda 15 suka mutu nan take yayin da sauran suka mutu a asibiti.

Shi ma wannan kisa ya ɗaga hankalin mutane tare da janyo suka daga ɓangarori daban-daban na ciki da wajen jihar.

Rahotanni a lokacin sun ce matashin mai shekara 38 ya cinna wutar ne sanadiyyar rikici da yake yi da wani ɗan’uwansa a kan rabon gado.

A watan Mayun 2025 ne dai babbar kotun Musulunci da ke jihar Kano ta yanke wa mutumin mai suna – Shafiu Abubakar- hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunsa da laifin da kashe masallatan.

ƙona kishiyoyi biyu a gidansu a Tudun Yola

A ranar 13 ga watan Nuwamban 2025 wasu mutane da ba a san kowa su wane ba, suka haura gidan wasu matan aure (uwargida da amarya) a unguwar Tudun Yola, inda suka halaka su tare da ƙona gawarwakinsu.

Shi ma wannan lamarin ya ɗaga wa al’ummar jihar hankali kasancewar shi ma ya faru ne da tsakar rana, lokacin da maigidan baya nan kuma babu zirga-zirgar mutane a unguwar.

Cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar a lokacin faruwar lamarin, ta ce tana cikin bincike domin farauto waɗanda ake zargi.

‘Yan sandan sun ce sun gano wasu wayoyin hannu guda biyu – da suke tsammanin na waɗanda suka aikata laifin ne.

Sai dai bayan kisan baya-bayan nan na ranar Asabar, ‘yan sandan sun ce mutanen da suka kama na da alaƙa da kisan matan na unguwar Tudun Yola.

Rahotanni daga jihohi daban-daban, musamman Kano da wasu sassan Arewa, na nuna cewa mafi yawan irin waɗannan laifuka na da nasaba da rikicin iyali, hassada, kishi, matsalar kuɗi, shaye-shaye, ko kuma rashin jituwa tsakanin ma’aurata da ‘yan uwa. Duk da yawaitar kama waɗanda ake zargi da aikata laifukan, har yanzu ba a taɓa zartar da hukuncin kisa kai tsaye ba a kan fitattun shari’o’in da suka ɗauki hankalin jama’a.

Shari’o’in da suka fi ɗaukar hankali

ɗaya daga cikin shari’o’in da suka fi ɗaukar hankali shi ne na kisan ɗalibar nan Hanifa Abubakar a Kano, inda aka kama wani malamin makaranta da wasu mutane bisa zargin sace ta tare da kashe ta. Duk da shari’ar ta ɗauki lokaci mai tsawo a kotu, har yanzu al’umma na jiran hukunci na ƙarshe, abin da ya janyo tambayoyi kan jinkirin shari’a da tasirinsa ga hana aikata laifi.

Haka kuma, ana ci gaba da sauraron shari’ar wani ɗan ƙasar China da ake zargi da kashe wata ‘yar Kano a cikin wani lamari da ya janyo ce-ce-ku-ce, inda al’umma ke fargabar cewa bambancin ƙasa ko matsayi na iya janyo sassauci a hukunci. Lamarin ya ƙara tayar da hankalin jama’a kan buƙatar adalci ba tare da nuna bambanci ba.

Masana harkokin shari’a da na zamantakewa na ganin cewa jinkirin shari’a da rashin hukunci mai tsauri na ƙara bai wa masu aikata laifuka ƙwarin gwiwar aikata kisan gilla, ganin cewa shari’o’in kan ɗauki shekaru ba tare da kammalawa ba. Sun jaddada cewa hukunci mai sauri da adalci na daga cikin manyan hanyoyin daƙile laifuka a kowace al’umma.

Kira ga hukumomi

A ɓangaren al’umma kuwa, malamai da shugabannin gargajiya na kira da a ƙara wayar da kan iyalai kan haƙuri, sulhu, da neman shawara kafin rikici ya rikiɗe zuwa tashin hankali, tare da kulawa da matsalolin taɓin hankali da shaye-shaye da ke ƙara dagula zaman lafiya.

Sai dai a gefe guda, masana shari’a sun bayyana cewa dalilin da ya sa ba a aiwatar da hukuncin kisa cikin gaggawa a Nijeriya ya samo asali ne daga tsarin doka da kundin tsarin mulki. A ƙarƙashin doka, duk wanda aka yanke wa hukuncin kisa yana da haƙƙin ɗaukaka ƙara zuwa ƙotun ɗaukaka ƙara da Kotun ƙoli. Wannan tsari kan ɗauki shekaru da dama, musamman idan lauyan wanda aka yanke wa hukunci ya ci gaba da shigar da ƙara a matakai daban-daban.

Bugu da ƙari, ko bayan an kammala dukkan shari’o’in ɗaukaka ƙara, hukuncin kisa ba zai tabbata ba sai gwamnan jiha ya sanya hannu a takardar aiwatar da hukuncin, wato death warrant. Sai dai a aikace, gwamnonin jihohi da dama kan guji sanya hannu, saboda matsin lamba daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, dalilan siyasa, ko kuma tsoron yiwuwar kuskuren shari’a.

ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam na jaddada cewa hukuncin kisa hukunci ne da ba juya shi, inda idan aka kashe mutum daga baya aka gano ba shi da laifi, ba za a iya gyara kuskuren ba. Wannan ra’ayi ya sa gwamnatoci da kotuna ke taka-tsantsan, musamman a ƙasar da ake fama da matsalolin bincike, shaidu marasa inganci da kuma zargin cin hanci a wasu matakan shari’a.

Sai dai duk da waɗannan dalilai, jama’a na ganin cewa rashin aiwatar da hukunci cikin lokaci na ƙara ƙarfin gwiwar masu aikata kisan gilla. A cewarsu, idan mai laifi ya san cewa shari’a za ta ɗauki shekaru masu yawa, kuma hukuncin kisa na iya zama ba a aiwatar da shi ba, hakan na rage tsoron doka da hukunci.

Masana tsaro sun yi gargaɗin cewa wannan yanayi na iya ƙara dagula zaman lafiya, musamman a yankunan da ke fama da talauci da ƙarancin ilimi, inda mutane ke ganin ɗaukar doka a hannu a matsayin hanya mafi sauri ta warware sabani.

A ƙarshe, al’umma, ƙungiyoyin farar hula da masana shari’a sun yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi, tare da ɓangaren shari’a, da su ɗauki matakai kamar: Hanzarta shari’o’in kisan kai ta hanyar ƙirƙirar kotuna na musamman, ƙarfafa binciken ‘yan sanda da amfani da shaidu na zamani da tabbatar da adalci cikin gaskiya ba tare da jinkiri ba, da kuma yin bitar manufofin hukuncin kisa domin tabbatar da cewa doka na taka rawar hana aikata laifi.

Sun jaddada cewa kare rayukan al’umma shi ne ginshiƙin kowace gwamnati, kuma duk wani tsari da ke barin jama’a cikin fargaba na buƙatar gyara cikin gaggawa. A cewarsu, idan har ba a ɗauki mataki ba, yawaitar kisan gilla na iya zama babbar barazana ga zaman lafiya da haɗin kan al’ummar Arewacin Nijeriya da ƙasa bakiɗaya.

By ukarofi