Gabanin zaɓen shugabannin majalisa… A na zargin ƙulla maƙarƙashiyar kama Yari

*Ƙungiya ta ja hankalin Tinubu da APC
*Kotu ta tsawaita wa’adin hana kama shi
*Za a ƙaddamar da Majalisa ta 10 ranar Talata

Daga NASIR S. GWANGWAZO da MAHDI M. MUH’D

Rahotanni sun nuna cewa, jami’an tsaron Nijeriya suna ƙulle-ƙullen kama tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari, su tsare shi har sai bayan ƙaddamar da Majalisar Dokokin Nijeriya ta 10 da za a yi ranar Talata mai zuwa, don tabbatar da cewa, bai samu damu tsaya wa takarar shugabancin Majalisar Dattawa ba.

Wannan zargin ya fito ne daga bakin Shugaban Ƙungiyar Matasan Yankin Arewa Maso Gabas (North East Youth Organisation Forum), Alhaji Abdulrahman Buba Kwaccham, yayin ganawa da manema labarai da ya kira a Abuja ranar Alhamis, 8 ga Yuni, 2023.

Ya ce, “mu na da yaqini da ƙishin-ƙishin daga ranar Lahadi akwai wasu ’yan takara da ake so a kama, don sun ƙi su janye takarar da suke yi. Ake so a kama su har sai an je zaɓe an ƙare a sake su.”

Idan za a iya tunawa, Wata babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsawaita dokar hana Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati, EFCC, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da sauran laifuffuka masu alaƙa (ICPC), da Sashen Tsaro na Ƙasa (DSS) tsare Sanata Abdul’aziz Yari bisa zargin sa da tafka wata almundahana.

Mai Shari’a Donatus Okorowo ne ya tsawaita wa’adin a ranar Alhamis bayan lauyan Yari, Michael Aondoaka, SAN, ya gabatar da buqatarsa ta baka bayan da aka yi zargin ana shirya maƙarƙashiyar kama shin, don hana shi tsaya wa takarar kujerar Shugaban Majalisar Dattawa.

Lamarin ya biyo bayan roƙon da lauyan hukumar EFCC, Gloria Ogbason da takwararta mai wakiltan ICPC, Kemi Odogun, suka gabatar na a ɗage shari’ar, domin ba su damar gabatar da martani ga buƙatar da Yari ya gabatar.

Da aka ci gaba da sauraren ƙarar, Aondoaka, ya sanar da cewa, an aika da dukkan waɗanda ake ƙara kamar yadda kotu ta umarce su.

Ogbason, wanda ya amince da karɓar ayyukan Yari a ranar 5 ga Yuni, ya ce har yanzu ba su gabatar da amsarsu ba.

Da yake tabbatar da maganar Ogbason, Odogun, wanda ya ce an yi wa ICPC aiki ne a ranar 6 ga watan Yuni, ya kuma nemi a ɗage zaman.

Aondoaka ya ce, duk da cewa ba ya adawa da aniyarsu ta mayar da martani ga buqatarsa, ya ce, “Za mu nemi a ba mu umarnin tsawaita wa’adin ne ranar 5 ga watan Yuni domin kotu ta ba da umarnin rage lokacin da za a nuna dalili.”

Babban Lauyan ya kuma bayyana cewa, akwai wata hujjar yin aiki a kan DSS, wanda ake tuhuma na 3 a cikin ƙarar, duk da cewa ba a gabatar da ita a kotu ba.

Obasun da Odogun ba su ƙi amincewa da buqatar Aondoaka na tsawaita odar.

Mai shari’a Okorowo, wanda ya ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Yuni, ya haramtawa EFCC, ICPC da DSS ci gaba da tsare Yari har sai sun bayyana dalilinsu a ranar da za a cigaba da zaman kotu.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, a ranar 13 ga watan Yuni ne za a ƙaddamar da majalisar dokokin ƙasar karo na 10 bayan sanarwar da shugaba Bola Tinubu ya yi.

A yayin da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan hukunci, Alhaji Abdulrahman Kwaccham, ya ce, “kotu ta bayar da oda akan kada a tava su. To, amma ana so a karya wannan doka, a kama su, wanda kuma idan aka yi haka, ba a yi wa ƙasa adalci ba kuma duniya tana ganin waɗannan abubuwan da ake son a yi.”

Ya yi ƙarin haske da cewa wannan shine dalilin kiran taron manema labarai da ya yi, inda ya ce, “maqasudin kiran wannan taro shine, akwai alamun ana son cutar da wasu ’yan takara, wanda kuma dimukraɗiyya ta ba wa kowa ’yancin ya nemi takara. Ana so a tursasa wa wasu ko a tsorata wasu, don a ba wa wasu dama.

“Don haka mu na kira ga Shugaban Ƙasa da kuma ita uwar jam’iyyar ta APC da sauran duka jam’iyyu da su janye maganar kawo ɗan takara, wanda ba shine wataqila majalisa ta ke so ba ko kuma al’umma suke so ba. Su bari a tafi a je a yi zaɓe mai adalci a zauren majalisa. Duk wanda Allah ya bawa, na ’yan Nijeriya ne kuma na Shugaban Ƙasa ne, kuma al’umma za su yaba da abinda aka yi maimakon a ɗauki wani a dinga ɗora wa al’umma, wannan bai dace ba! Wannan ba dimukraɗiyya ba ce.”

Ya cigaba da cewa, “ana so a yi amfani da wani abu ta bayan fage, don a muzguna musu, wanda kuma al’ummar Nijeriya ba za su lamunta ba, duniya ba za ta lamunta ba!

“Duk rashin adalci shi ya kawo fitintunun da muke ciki. Yana da kyau a matsayinsu na shugabanni, su kasance mutane ne masu adalci, masu tunani, masu kuma taimakon al’umma da cigaban Nijeriya, ba masu son wargaza Nijeriya ba!”
Alhaji Kwaccam ya ƙara da cewa, “yana da kyau jam’iyya ta samarwa da ’ya’yanta alƙibla, kuma kowane ɗan takara da jam’iyya ne ya kai matsayin da ya ke, amma mafita ita ce idan jam’iyya ta abinda ake yi ba daidai ba ne, to ba wai turasasawa za ta yi ba, sulhu ake nema a zauna a ce ga abinda ake son a yi.

“Amma waɗansu matakan da ake ɗauka a yanzu na tozartawa da cin mutunci, don a biya wa wasu buƙata, ba zai haifar wa jam’iyya ɗa mai ido ba a Nijeriya.”

Yayin da yake amsa tambaya kan matsayar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wannan badaƙala, sai Kwaccam ya ce, “a yadda na ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tsaya tsayin daka, ba na tsammanin akwai wanda zai kawo masa tarnaƙi idan ya zama Shugaban Majalsa, saboda niyyarsa ta raya Nijeriya, don Tinubu ya zo da kyakkyawar manufa.”

Ya ƙara da cewa, zaɓaɓɓun ’yan majalisar Nijeriya ba yara ba ne. Don haka ya dace a bar su su zaɓar wa kansu wanda suka ga ya dace ya shugabance su.

Tuni dai Magatakardar Majalisar Dokokin Nijeriya, Sani Tambuwal, ya bayyana cewa, za a ƙaddamar da majalisar ta 10 a ranar Talata 13 ga Yuni 2023 da ƙarfe 10:00 na safe.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Tambuwal ya ce, zavavvun sanatoci da zaɓaɓɓun ’yan Majalisar Wakilai za su ziyarci ɗakin taro na Majalisar Dattawa mai lamba 231 da ɗakin taro na Majalisar Wakilai 301, tare da kwafin qa’idojin aikinsu, da takardun shaida na dawowa da ingantattun katunan shaida don rajista ranar Litinin, 12 ga Yuni, da ƙarfe 10:00 na safe.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Saboda gyaran da ake yi a majalisun biyu, zaɓaɓɓun ‘yan Majalisar Dattawa da zaɓaɓɓun ‘yan Majalisar Wakilai za su halarci bikin,” in ji sanarwar.

Tambawal ya ƙara da cewa, zaɓaɓɓun sanatoci da zaɓaɓɓun ’yan majalisar ne kaɗai za a ba su damar shiga zauren majalisar.