Yadda jaruma Rashida Maisa’a ta jagoranci kai wa Aisha Buhari ziyarar karramawa a Daura

Daga AISHA ASAS

Larabawa na wani karin magana, “lli kulli bidayyatin nihaya” Bahaushe kuwa na cewa, komai ya yi farko zai yi ƙarshe. A daidai lokacin da wa’adin mulkin shugaba Muhammadu Buhari ya kawo ƙarshe, wasu da dama daga cikin alkhairan da makusantanshi ke yi suka tsaya tare da shi, don haka ɗinbin mutane suka shiga alhenin rashin majingin da suke jingina da shi a tsakanin ahalinsa ko makusantansa.

A ranar 29 ga watan Mayu ne Nijeriya ta yi sabon ango, wanda hakan na nufin karɓar ragamar mulkin ƙasa daga hannun Muhammadu Buhari zuwa ga sabon Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu. Da wannan ne tsohon shugaban qasa da iyalansa suka kwashe kayansu don komawa mahaifarsa da ke Daura da zama, domin ba wa sabon shugaban ƙasa damar maye gurbinsa na tsayin shekaru huɗu.

Masu iya magana suna cewa, alheri gadon barci, kuma duk ɗan halak ba ya manta shi idan an yi masa. Yayin da ka ke aikata wani aikin alkhairi ga wasu mutane, za su kasance masu godiya da kuma tunawa da shi a cikin kowanne hali.

Uwar gidan tsohon shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, na ɗaya daga cikin matan da suka taka rawa ga al’ummarta a lokacin da suke mulki, domin ta zama sanadin ciyar da ɗimbin mutane a ƙarƙashin gidauniyarta mai suna ‘Futureassured’. Da yawa sun amfana da tallafin wanda ta ke amfani da wasu mutane da ke da gidauniya don isar da tallafin ga mabuƙata.

Da wannan ne wasu daga cikin waɗanda suka more wannan gidauniya suka yi shiri ƙarƙashin jagorancin jaruma a masana’atar finafinai ta Kannywood, kuma ɗaya daga cikin matan da ke bada tallafi ga mabuƙata, Rashida Adamu, wadda aka fi sani da Maisa’a, don kai wa uwar gidan tsohon shugaban qasa Hajiya Aisha Buhari, ziyara a gidan mijinta da ke Daura, da nufin nuna godiya da kuma karramata kan namijin ƙoƙarin da ta yi wa al’umma a tsayin shekaru takwasda suka yi a mulki.

A cewar Jarumar, wannan ziyara ce ta nuna godiya da kuma jinjina ga matar ta tsohon shugaban qasa, kan irin damar da ta bata na zama ɗaya daga cikin waɗanda wannan tallafi na gidauniyar tata ke zuwa hannunsu don isa ga mutane.

“Sakamakon dama da matar tsohon shugaban ƙasa Hajiya Dakta Aisha Muhammad Buhari, ta ba ni ƙarƙashin gidauniyarta ta ‘Futureassured’, mun yi aiki lafiya, kuma mun kammala lafiya. Da wannan ne muka kai mata ziyarar jaddada goyon baya, mun kuma karramata akan kasancewarta mace ta farko da ta yi irin wannan aikin taimako mai yawa a Nijeriya,” a cewar Maisa’a.

Jarumar ta ƙara da cewa, “sun ji daɗin ziyar tawa, domin Baba Buhari ya sanya min albarka, kuma ita ma ta sanya min albarka, sannan na ƙara jaddada goyon baya na gare su, Ina tare da su ɗari bisa ɗari.”

Rashida ta ƙara da bayyana saƙon tsohon shugaban ƙasa da matarsa gare ta, waɗanda suka bata tabbacin harkar tallafa wa al’umma ba ta zo ƙarshe ba kamar yadda wa’adin mulkinsu ya zo.

“Sun tabbatar min harka ta tallafi idan aka tashi wadda ba daina ta aka yi ba, za mu ci gaba daga nan har ƙarshen rayuwarmu, da yardar Allah.”

Daga ƙarshe jarumar ta bayyana godiyarta ga irin tarbar da suka samu, kuma ta yi wa tsohon shugaban qasa Muhammadu Buhari da mai ɗakinsa Hajiya Aisha Buhari fatan alkhairi da kuma taya su murnar kammala wa’adin mulkinsu na shekaru takwas. Sannan ta yi addu’ar alkhairi gare su a sauran rayuwar da ta rage masu.

Daga cikin waɗanda suka kai wannan ziyarar akwai Fauziya D. Sulaiman, a ƙarƙashin gidauniyarta ta ‘Creative Helping Needy Foudation’, wadda ta jima tana karɓar tallafin kayan abinci don rabawa da ma taimakon marasa lafiya. Sai Hajiya Umma Sulaiman ‘Yan Awaki, marubuciya da ta ke jan ragamar gidauniyar ‘Women and Children Dream Foundation’, sai jaruma Mansura Isa, Zuwairiyyah Adamu Girei da sauransu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *