Gbajabiamila ya yi murabus daga Majalisar Wakilai

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya yi murabus daga Majalisar Wakilai domin kama aiki a matsayin sabon Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Ƙasa.

An gabatar da wasiƙar tasa ga Majalisar ne inda Shugaban Majalisar, Tajudeen Abbas, ya karanto.

Tun farko rahotanni sun nuna dole Gbajabiamila ya sauka daga matsayin shugabancin majalisar domin ba shi damar fuskantar aikin sabuwar gwamnati.

Da ma dai wasu ‘yan ƙasar sun nuna damuwa kan yadda yake gudanar da muƙamai guda biyu a kansa, wato a matsayinsa na Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa da kuma ɗan majalisa wanda har an rantsar da shi tare da takwarorinsa a ranar Talatar da ta gabata.

Yanzu tun da ya miƙa wasiƙar barin majalisar a matsayin mai wakiltar Surulere 1, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), za ta gudanar da zaɓen cike gurbi don cike gurbin da Gbajabiamila ya bari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *