Gwamnatin Kano ta rushe shataletalen Gidan Gwamnati

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Engr. Abba Kabir Yusuf, ta ci gaba da aikin rusau da take gudanarwa a cikin garin Kano,

Inda a ranar Talata da daddare aikin rusau ɗin ya dira kan shataletalen da ke daura da Fadar Gwamnatin jihar.

Bidiyon lamarin da ya karaɗe gari, ya nuna yadda motar rusau ɗin ta yi rugu-rugu da randabawul ɗin.

Rusau da Gwamnatin Abba Kabir Yusurf ta Jam’iyyar NNPP ke ci gaba da yi a jihar na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce tsakanin ɓangarorin da ke ganin dacewarsa da kuma masu ganin rashin kyautatuwar hakan, lamarin da wasunsu ke kallon bi-ta-da-ƙulli ne ga gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da ta gabata.

Da ma dai tun kafin hawansa, Gwamna Abba ya yi alƙawarin rusa gine-ginen da aka yi su ba bi sa ƙa’ida ba, da kuma ƙwato filaye da kadarorin gwamnati da Gwamnatin Ganduje ta cefanar ba bisa ƙa’ida ba.

Ana zargin Gwamnatin Ganduje da yin gaban kanta da kuma son zuciya wajen sayar wa muƙarrabai da iyalai kadarorin gwamnati a kan kuɗin da bai taka kara ya karya ba, da kuma cin filaye da yin gine-gine a wuraren da bai dace ba, zargin da ta musanta.

Tun bayan hawan Abba ya ƙaddamar ayyukan rusau, lamarin da ya fusata Ganduje, har ya ce da sun haɗu da uban gidan Abba, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a Fadar Shugaban Ƙasa da zai iya gaura masa mari.

Ganduje ya faɗi hakan ne a Fadar Shugaban Ƙasa, lokacin da ya kai ƙarar Abba ga Shugaba Tinubu a ranar Juma’a da ta gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *