Gwamna Bala ya naɗa Farfesa Fatima Tahir Muƙaddashiyar Shugabar Jami’ar Gadau

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya naɗa Farfesa Fatimah Jafar Tahir a matsayin Muƙaddashiyar Shugabar Jami’ar Sa’ad Zungur ta jihar dake Gaɗau (SAZUG).

Wata takardar jawabi da aka raba wa manema labarai ɗauke da sa hannun kwamishinan ilimi na jiha mai baring ado, Dokta Aliyu Usman Tilde ya fitar ta ce, “Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayyana naɗin Farfesa Fatima Tahir a matsayin muƙaddashiyar shugabar Jami’ar Sa’ad Zungur dake da mazauni a garin Gadau (SAZUG) ta jihar Bauchi.

“Farfesa Fatima Tahir ƙanwa ce ga marigayi Talban Bauchi, Dokta Ibrahim Tahir. Ta kasance ta ɗaya daga cikin fitattun ma’abuta ilimi guda 12 da suka nemi wannan kujera yayin da aka yi masu jarrabawar bin ƙwaƙƙwafi (Interview) kimanin kwanaki arba’in da biyar (45) da suka gabata. Ina gaya wannan ‘yar uwa murna, haɗi da ita Jami’ar jiha ta Sa’ad Zungur (SAZUG),” inji Tilde.

Farfesa Fatimah Jafar Tahir dai farfesa ce akan ilimin ‘Microbiology’ wacce kuma kafin wannan sabon naɗi nata, ita ce Muƙaddashiyar shugaba (VC) ta Jami’ar Soji ‘Nigerian Army University’ (NAUB) dake garin Biu ta jihar Borno. An shaidar itace mace farfesa ta farko a cikin Ƙaramar Hukumar Bauchi ta jihar Bauchi, kuma ita ce mace farfesa ta farko daga Jihar Bauchi da Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) ta yaye.

An haife ta a ranar 8 ga watan Fabrairu na shekarar 1966, kuma ta kammala dukkan karatunta na boko a garin Bauchi, daga firamare, sakandare da kuma gaba da sakandare. Nasarorin ilimi dabam-dabam data samu a da’irar garin Bauchi ya sanya aka yi mata laqabin “Ƙirar Bauchi”.

Dalilin maƙala mata wannan laƙabi shi ne, ta gama koyon ilimin ta na gaba da sakanadare duka a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU), wata daga karatun digirin farko, na biyu har zuwa digiri na uku. Kazalika ɗaukacin karatun ilimin ta na sana’a ta gudanar da shine a ATBU, Bauchi, inda ta fara daga mataimakin wanda ya kammala karatun digiri, ta ɗaukaka har ya zuwa matsayin farfesa mai ilimin ‘Microbiology’.

Ta fara ne a shekara ta 1991 a matsayin mataimakiya ga wanda ya kammala karatun digirin farko ta nausa zuwa malamin jami’a mataimaki (Assistant lecturer) a shekara ta 1994 bayan ta kammala karatun digiri na biyu.

Daga wannan gurbi sai ta samu ƙarin girma zuwa Malamar Jami’a 11, Malamar Jami’a 1, Babbar Malamar Jami’a, kuma a shekara ta 2009 ta kasance a matsayin mai ilimin farfesa.

Fatima dai tana da aure kuma uwa mai yara. A shekara ta 2011, wata Ƙungiya ta karrama ta a matsayin farfesa mace ta farko a cikin ƙaramar hukumar Bauchi.

Farfesa Fatimah Tahir tana da wallafe-wallafe da mujallu kimanin guda talatin, kuma ta kasance mai duba karatun masu neman digiri na biyu dana uku a yayin da take jami’ar ta ATBU.

Fatima mamba ce a Tarayyar Ma’abuta Ilimin ‘Microbiology’ (NSM) da Cibiyar Kimiyyah da Fasahar Abinci ‘Nigerian Institute of Food Science and Technology (NIFST)’ da Cibiyar Amurka ta Masu Ilimin ‘Microbiology (SFAM)’ da sauransu.