Fadan ‘yan bindiga a kan bazawara ya yi sanadin mutuwar mutum 64 a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Al’ummar garin Mutunji a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya suna cikin halin zullumi da tashin hankali, bayan asarar rayuka mafi muni da garin bai taɓa ganin irin sa ba.

Rahotanni daga garin sun ce aƙalla mutum 64 ‘yan garin ne suka rasa rayukansu bayan da wani jirgin soja ya jefa bam a wani waje da ‘yan bindiga suka yi mafaka.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa saboda tsaro ya tabbatar wa BBC cewa dukkan waɗanda suka mutun maza ne, mafi yawan su ƙananan yara, sai kuma matasa da tsofaffi.

“An yi asarar rayukan da ba a tava samun yawan hakan ba a rana guda a garin namu kuma baya ga waɗanda suka rasa rayukansu da dama sun jikkata,” ya ce.

Ganau ɗin wanda shi ma ya rasa ‘yan uwansa da dama, ya ce an kai waɗanda suka jikkatan asibitin garin Ɗan Sadau da na Gusau ana duba su.

“Mutum 17 suna asibitin Ɗan Sadau su kuma 12 da suka fi jin munanan raunuka suna asibitin Gusau duk ana kula da su.”

Jama’ar garin na Mutunji sun ce kwana shida da suka wuce ne wasu dabobin ‘yan bindiga biyu a garin Randa suka yi rigima a kan wata bazawara “da kowa ke so”.

A kan hakan ne aka samu hatsaniya tsakanin su a cikin daji har aka kashe mutum biyu.

Ganau ɗin nan ya ce wa BBC “to daga nan ne sai wani babban ɗan bindiga ana ce masa Damina, ya ce ai mutanen garin ne suka kashe masa yara a don haka sai ya kwashe ‘yan garin har mutum 174, a ciki ya kashe mutum 20.

“A yanzu haka kuma wasu fiye da 150 suna hannunsa. Kuma majiyoyi masu ƙarfi sun shaida mana cewa kisan gilla ya yi wa mutane 20 ɗin.

“Bayan nan ne sai Damina ya ce wa mutanen garin Randa ya yi binciken da ya kamata ya yi kuma ya gano mutanen garin Malele ne suka kashe masa yaran,” ya ce.

Jama’ar garin sun kuma ce hakan ya sa aka kai wa mutanen Malele hari, a yayin hakan ne kuma suka yi wa sojoji kwanton vauna har suka kashe tara daga cikin su, suka kuma jikkata huɗu da a yanzu haka suke asibitin Ɗan Sadau.

Wata majiya daga rundunar sojin ta tabbatar wa BBC cewa sojoji 12 ne suka mutu amma su ma ‘yan bindigar da dama sun rasa rayukansu.

Wannan abu da ‘yan bindigar suka yi ne ya sa sojojin suka nemi ɗauki daga sojojin sama, su kuma ɓarayin lokacin suna neman mafaka sai suka faɗa garin garin Mutunji.

‘Kazalika sun ce hakan ne ya sa sojin saman suka jefa bam a yankin ta jirgin yaƙin da ya gansu, “wanda tashin bam ɗin ne ya hallaka ‘yan bindigan da kuma mutanen gari har 64,” kamar yadda ‘yan garin suka ce.

Sai dai duk da cewa rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da cewa ta yi nasarar kashe ‘yan bindiga da dama, amma ba ta ce harin ya kashe fararen hula ba.

Harin jirgin yaqin dai ya sa an yi asarar duk wani abu da ke wajen da bam ɗin ya tashi, kama daga gidaje zuwa shaguna baya ga mutanen da suka mutu kamar yadda rahotanni suka ce.

A yanzu haka mutanen garin da aka sace jama’arsu 174 ɗin sun ce tuni suka fara neman hanoyoyin yin sulhu don a dawo musu da su ba tare da an sake kashe ko guda ba.

Rahotannin wasu kafafen yaɗa labarai a Nijeriya sun ruwaito nasarar da rundunar sojin ƙasar ta yi tun daga ranar Asabar a Jihar Zamfara.

Sojojin sun ce sun samu nasarar kashe ‘yan bindiga da yawa bayan da rikici ya yi ƙamari a garuruwan Malele da Maigoge da ‘Yan Sawayu da Ruwan Tofa da Mai Awaki da Zama Lafiya da duka suke ƙarƙashin gundumar Mutunji a ƙaramar hukumar mulki ta Ɗan Sadau.

Jaridar intanet ta PRNigeria ta ce wata majiyar sirri daga ma’aikatar tsaro ta bayyana mata yadda dakaru suka ƙaddamar da jerin hare-haren sama kan dabobin ‘yan bindiga daban-daban a yankin.

An daɗe ana fama da rikice-rikice a Jihar Zamfara amma hukumomi na cewa suna ƙoƙarin shawo kan lamarin.

“Wasu ‘yan bindiga da suka shiga garin Mutunji don neman mafaka daga harin sama na sojoji sun gamu da gamonsu. Bayan da aka tabbatar rayuwar mutanen ƙauyen ba ta cikin hatsari sai aka far wa ‘yan bindigar da ruwan wuta daga sama.

“Hakan ya sa an yi nasarar hallaka ‘yan bindiga fiye da 40 da suka vuya a ƙauyen. Wasu fararen hula kaɗan sun ji raunuka amma ba munanan raunuka ba ne,” a cewar majiyar sojin, kamar yadda PRNigeria ta ambata.

Wasu mazauna yankunan dai sun bayyana jin daɗinsu kan nasarar da sojojin suka samu.

Wani matashi ya shaida wa PRNigeria cewa ya kamata sojoji su ci gaba da ƙoƙari don hana ‘yan bindigar sakat da kawo zaman lafiya a yankin.