Qausain TV ta ƙulla alaƙa da tashar France 24

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar tashar talabijin ta duniya, wato France 24 ta ƙulla alaƙar aiki tsakaninta da Qausain TV dake nan Nijeriya.

Shugaban Qausain TV, Malam Nasir Musa Idris (Albani Agege) ne ya bayyana haka a wannan makon, jim kaɗan bayan amsa gayyatar da tashar ta France 24 ta yi masa.

Nasir Albani wanda yanzu haka yana ƙasar Faransa domin kammala shirye-shiryen fara aikin, ya ce: “A halin yanzu Ina ƙasar Faransa, bayan da muka samu tagomashin gayyata zuwa birnin Faris (Paris), inda babban gidan talabijin mai ƙololuwar daraja wato France 24 ya ba ni kujerar zama ɗaya daga cikin jajirtattun masu gidajen talabijin na duniya dake da alaƙa da su.”

Ya ƙara da cewa wannan wani tafarki ne na haɓɓaka daraja tare da watsa martabar harshen Hausa a faɗin duniya.

“Lallai alaƙar zumunci mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin Qausain TV da sahar France 24, kuma haɗaka ce mai matuƙar alfanu da sauƙi da za ta zama gadar sadar da Hausawan duniya, domin ƙara sanin abubuwan da ke faruwa a duniya a sauƙaƙe.

Qausain TV dai tashar talabijin ce da ta yi fice a Nijeriya wajen yaɗa shirye-shirye masu ƙayatarwa cikin harsunan Hausa, Turanci da kuma Larabci.