CBN ya tabbatar wa Majalisar Wakilai odar sabbin takardun Naira miliyan 500

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ce, an yi odar sabbin takardun kuɗi har na Naira miliyan 500 kuma za a buga su nan ba da jimawa ba.

Mataimakiyar Gwamnan Bankin CBN Mai Kula da Daidaiton Harkokin Kuɗaɗe, Aisha Ahmad, ta bayyana hakan a yayin da ta bayyana a gaban majalisar a matsayin wakiliyar gwamnan bankin, Godwin Emefiele, bayan goron gayyatar da majalisar ta aike masa.

A watan Nuwamba ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da wasu takardun kuɗi na Naira 1000 da N500 da kuma N200 da aka yi wa kwaskwarima.

Tun a ranar 15 ga watan Disamba kuɗaɗen suka fara yaɗuwa, amma ana ta ƙorafin rashin isasshen adadin da ake samu a bankunan ajiya.

Ana kuma sa ran ’yan majalisar za su ba wa Aisha, wanda ke wakiltar Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin ƙasar shawara kan sabuwar manufar cire kuɗi ta babban bankin ƙasar.

A halin da ake ciki kuma, babban bankin ƙasar CBN ya ƙara yawan adadin kuɗaɗen da za a iya cirewa duk mako ga duk kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane zuwa Naira 500,000 da kuma Naira miliyan 5.

Wannan cigaban yana ƙunshe ne a cikin wata wasiqa da aka aika wa bankuna a ranar Laraba, 21 ga Disamba, 2022.

Wannan cigaban ya zo ne makonni biyu bayan da CBN ya rage adadin kuɗaɗen za a iya cirewa duk mako a kan kuɗi Naira 100,000 da na kamfanoni zuwa N500,000.