Kotu ta yanke wa Doyin Okupe shekaru biyu a gidan yari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Litinin ne wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Doyin Okupe, tsohon babban mataimaki na musamman, SSA kan harkokin yaɗa labarai ga tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, Doyin Okupe, ɗaurin shekaru biyu a gidan yari.

Mai shari’a Ijeoma Ojukwu, a hukuncin da ta yanke, ta samu Okupe da laifuka 26 daga cikin 59 da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC ta shigar a kansa kan laifin satar kuɗi.

Mai shari’a Ojukwu ya bayar da umarnin cewa tuhume-tuhume 26, waɗanda suka janyo wa Okupe zaman gidan yari na shekara biyu kowanne, za su gudana a lokaci guda.

Alƙalin kotun, ya bayar da zaɓin Naira 500,000 a kowanne daga cikin tuhume-tuhumen, wanda adadinsu ya kai Naira miliyan 13, wanda dole ne a biya kafin qarfe 4:30 na yamma a ranar.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, mata da ‘ya’yan Okupe sun nemi a yi masa sassauci bayan an yanke masa hukuncin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *