‘Yan bindiga sun kashe mutane 28 a Kudancin Kaduna

Daga SANI SHEHU LERE a Kaduna

Mutum 28 sun mutu, an jikkata wasu da dama a harin ‘yan bindiga a qauyukan Malagum 1 da Sokwong na Ƙaramar Hukumar Ƙaura ta Jihar Kaduna.

PRNigeria ta rawaito cewa Sakataren Ƙaramar Hukumar, Raymond Ibrahim, ya ce ‘yan bindiga sun far wa ƙauyen Sakwong ne da misalin ƙarfe 12 na dare kafin wayewar garin Lahadi, su na harbi kan mai uwa da wabi tare da cinna wa gidaje da dukiyoyi wuta.

Ya ce, “da safen yau muka dawo daga wurin muka ga gawarwaki tara, daga nan muka ƙarasa zuwa qauyen Malagum 1 inda ganau suka tabbatar mana cewa an kashe mutum 19.”

Raymond Ibrahim ya ce an kai harin ne kwana biyar bayan wani da aka kai a Malagum 1 aka kashe mutum huɗu.

Jami’in ya buƙaci mutanen su kwantar da hankalinsu, sannan ya roƙi gwamnati ta kawo ɗauki ga mutanen yankin da suka rasa muhallansu.

Wakilin PRNigeria ya tuntuvi Kakakin ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Muhammed Jalige, domin ƙarin bayani, amma bai amsa waya ba.