Aƙali ya hana ‘yan jarida sauraron shari’ar ‘yar Gwamna Ganduje, Asiya-Balaraba

Daga WAKILINMU

Alƙali Khadi Abdullahi Halliru na Kotun Shari’a a Kano, ya umarci ‘yan jarida su fita daga kotunsa don sauraron ƙarar da ‘yar gidan Gwamna Ganduje, Asiya-Balaraba Ganduje, ta shigar kan batun aurenta.

A cewar Alƙalin, duk da dai babu wanda ya fi wani a gaban doka, sai dai wannan shari’ar, shari’a ce da babu buƙatar a yaɗa ta bisa la’akari da ƙimar waɗanda ta shafa.

Jaridar Daily Nigerian ta kalato cewar, Asiya-Balaraba ta shigar da ƙara kotu ne inda ta buƙaci a raba aurenta da maigidanta Inuwa Uba, saboda wai ta gaji da auren.

Sai dai kuma, mijin ya ce shi dai yana son matarsa, don haka ua buƙaci kotun ta ba shi lokaci a kan ya koma ya rarrashi matar tasa don ta janyen kudurinta a kotu.

Daga bisani, Alƙalin ya bai wa mijin mako biyu a kan ya je ya san yadda zai shawo kan matarsa, kana ya ɗage shari’ar zuwa 5 ga Janairu don yanke hukunci.

Majiyarmu ta ce, shekarun baya Asiya ta samu akasi da iyayenta saboda goyon bayan maigidanta wanda suka zarge shi da tatsar musu dukiya.

Majiya ta kusa da ahalin ta shaida wa Daily Nigerian cewa, bayan da ta fuskanci matsi ta juya wa mijin nata baya, an ga jami’an tsaro sun shiga gidansu da ke Technical Staff Quarters inda suka kwashi wasu muhimman takardu masu nasaba da dukiyar Uba.

Majiyar ta ƙara da cewa, takardun sun shafi har da na kamfanin sarrafa shinkafa da ke hanyar Kano zuwa Zariya da sauransu.