Ana cigaba da alhinin rasuwar Sarkin Sudan na Wurno, Shehu Malami

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A na cigaba da alhinin rashin shahararren jami’in diflomasiyya kuma Yariman Sakkwato, Alhaji Shehu Malami, wanda ya rasu yana da shekara 85 a duniya.

Marigayi tsohon Jakadan Nijeriya a Afirka ta Kudu (lokacin Marigayi Janar Sani Abacha), ya rasu ne a ranar Litinin a Ƙasar Masar.

Marigayi Sarkin Sudan na Wurno, haifaffen gidan sarauta ne na Sarkin Musulmi, wanda kuma ya taso a gidan Sarkin Musulmi Abubakar, ya riƙe matsayin Babban Sakataren Sarkin Musulmi a shekarar 1960.

Ya yi karatu a makarantu daban-daban da suka haɗa da firamare a Sakkwato, Makarantar Lardin Kano, Makarantar Midil ta Sakkwato, Makarantar Lardin Katsina da Makarantar Lardin Bida.

Marigayin kuma Yariman Sakkwato, ya samu shaidar kammala karatunsa a Kwalejin Fasaha ta North Davon dake Barnstaple, sannan ya halarci Middle Temple. A lokacin yana Ingila ya shiga harkar haɗakar Jam’iyyar Peoples Congress reshen Landan tare da Umaru Dikko.

A cikin 1970, ya kasance mamba na Kwamitin Tsarin Mulki da Majalisar Zartaswa.

Ya yi aiki a hukumomi da kamfanoni da dama da suka haɗa da Costain West Africa, Nigeria Industrial Development Bank, NIDB, Tannery; Nigeria Pipes Ltd; Shempat, Patterson Zachonis, PZ, Japan Petroleum Company, da Indo-Nigeria Merchant Bank.

Shi ne tsohon Maigarin Wurno, Ƙaramar Hukumar Wurno a Jihar Sakkwato kafin a mayar da ita zuwa masarautar Dange a shalkwatar qananan hukumomin Dange/Shuni a matsayin Sarkin Baura wanda Marigayi Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki (Sarki na 18) ya naɗa sa.

Bayan muqamin Maigarin Wurno, marigayin ya kuma kafa kamfanoni a ƙaramar hukumarsa don sama wa matasa ayyukan yi, wanda ya haɗa da Zaki Bottling Company da ke sarrafa ruwan lemu da kayan shaye-shaye da Wurno Plastic Limited da Wurno Construction Materials wanda aka fi sani da WUCOMAT.

Hamshaqin ɗan kasuwar kafin rasuwarsa ya kuma tava yin aiki da kamfanin wutar lartarki na Abuja AEDCO.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana rasuwar basaraken na Sakkwato a matsayin babban rashi, ba ga iyalansa ba ka ai har da gwamnatin Nijeriya da kuma ɗaukacin al’ummar jihar Sakwato.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu, ya fitar, Shugaba Buhari ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalai da kuma ‘yan uwan marigayin.

Yanzu haka dai ’yan Nijeriya daga ciki da wajen ƙasar na cigaba da turuwar miƙa ta’aziyyar rasuwar Yariman na Sakkwato.