Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya karɓi baƙuncin matar nan Hauwa’u tare da ‘ya’yanta wanda ayyukan ‘yan bindiga suka jefa cikin mawuyacin hali a jihar.
Cikin wani faifan bidiyon da aka yaɗa kwanan nan, an ga yadda Hauwa’u tare da ‘ya’yanta suna cin ciyawa a matsayin abinci don tsira da rayuwarsu.
Mai magana da yawun Gwamna Lawal, Sulaiman Bala Idris, ya faɗa a ranar Alhamis cewa, halin da matar da ‘ya’yanta suka tsinci kansu ya nuna akwai buƙatar gaggawa wajen maganace silar faruwar hakan da kuma taimaka wa rayuwarsu.
Ya ƙara da cewa, baƙuncin matar da ‘ya’yanta da Gwamnan ya karɓa alama ce ta kyakkyawan ƙudurin da Gwamnan ke da shi na karewa da kuma kyautata rayuwar ‘yan jihar baki ɗaya.
Sanarwar da Bala Idris ya fitar ta ce, “A yau Gwamna Dauda Lawal ya karɓi Hauwa’u Halliru wadda ta rasa komai nata sakamakon ayyukan ‘yan fashin daji.
“Gwamna Lawal ya tabbatar da himmarsa wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar tare da miƙa ta’aziyyarsa ga ɗaukacin waɗanda suka rasa nasu a sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda.”
Sanarwar ta ƙara da cewa, Gwaman ya bai wa Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na Jihar umarnin tabbatar da an saka ‘ya’yan Hauwa’u a makaranta nan take ƙarƙashin ɗaukar nauyin gwamnati.
Tare da kira ga hukumomin da lamarin ya shafa da su binciko ahali marasa galihu makamancin Hauwa’u a faɗin jihar domin ba su tallafin da ya dace.
A nasa ɓangaren, Comrade Salisu Umar, shugaban masu kare ‘yancin ɗan Adam a jihar, ya yaba da ƙoƙarin da Gwamna Lawal ke yi na kyautata rayuwar talakawansa.
