Mutuwar Farfesa Umar Shehu babban rashi ne ga Arewacin Nijeriya – Gwamnonin Arewa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta yi alhinin rasuwar Emeritus Farfesa Umaru Shehu, Farfesan Farfesa na kiwon lafiyar al’umma na Arewacin Nijeriya, ya rasu ranar Litinin yana da shekaru 97 a duniya.

Gwamnan jihar Gombe kuma shugaban ƙungiyar, Muhammadu Inuwa Yahaya, a cikin saƙon ta’aziyyarsa, ya bayyana Marigayi Umaru Shehu a matsayin haziƙi kuma ƙwararre na gaskiya wanda rasuwarsa ta haifar da gurbi mai tarin yawa a fagen ilimi da shugabanci a Nijeriya.

A cewar Gwamna Yahaya rashin Farfesa Emeritus Umaru Shehu ya haifar da babbar matsala, ba wai ga iyalansa, jihar Borno da Jami’ar Maiduguri kaɗai ba, har ma da ɗaukacin yankin Arewacin Nijeriya, da kuma al’ummar duniya baki ɗaya.

Ya lura cewa Shehu ba suna kawai ba ne, ma’ajiya ce ta hikima, fitilar ilimi, kuma mai nuna sadaukarwa ga al’ummarsa da ƙasarsa.

Shugaban ya ƙara da cewa, irin rawar da Farfesa Umaru Shehu ya yi a jami’o’i da dama, da suka haɗa da Jami’ar Nijeriya, Nsukka (UNN), Jami’ar Ahmadu Bello, (ABU), Zariya, Jami’ar Maiduguri, da kuma rawar da ya taka a matsayin wanda ya kafa Ƙungiyar Dattawan Borno da Gidauniyar Tarihi da Al’adu ta Kanem Borno sun bar giɓi a tarihi a cikin al’umma.

Ya ce irin gudunmawar da Farfesa Shehu ya bayar a matsayinsa na Shugaban Kwalejin Kimiyya ta Nijeriya da kuma matsayinsa na Farfesa Emeritus na Kiwon Lafiyar Jama’a a Jami’ar Maiduguri, haƙiƙa ya ƙara wa al’umma basira.

A cewarsa, karramawar da Umaru ya samu a duniya a matsayin Babban Editan Mujallar Likita ta Burtaniya ya nuna iyawarsa na musamman.

Shugaban NSGF ya yi imanin cewa lallai Arewa ta rasa ɗaya daga cikin haziƙan masu basira da ilimi mai daraja a duniya.

Ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Borno, da Jami’ar Maiduguri, da al’ummar ƙasa bisa wannan babban rashi da aka yi.

Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya gafarta masa kurakuransa, ya saka masa da Aljannar Firdausi.

By Editor