Gwamna Wike ya bada tallafin biliyan N2.1 ga jihohi huɗu yayin da jiharsa ke cikin ƙunci

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ba da tallafi aƙalla Naira biliyan 2.1 ga jihohi Nijeriya guda 4 a cikin watanni 15 kacal. 

Rahotannin sun bayyana cewa, Gwamnan ya raba tallafi ne a tsakanin watan Janairun shekarar 2021 zuwa watan Oktoban 2022.

A watan Janairun shekarar 2021 ne dai Wike ya ba da gudunmowar Naira miliyan ga takwaransa na jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, don sabunta ginin Babbar kasuwar Sokoto wacce ibtilain gobara ya sabauta. 

A cikin watan Mayun dai shekarar dai ta 2021, gwamna Wike ya sake ba da gudunmowar wata Naira miliyan 600 a yayin taron buɗe asibitin koyarwa na   Akwa Ibom dake garin Awa na yankin ƙaramar hukumar Onna dake jihar Akwa Ibom.

Hakazalika, a cikin watan Fabrairun shekarar da muke ciki ta 2022 kuma, ya sake bayar da kyautar Naira miliyan 500 ga Jami’ar karatun likitanci ta jihar Bayelsa wacce take a garin Yenagoa, babban birnin jihar.

Sai kuma bayan watanni uku kuma, ya ba da kyautar Naira miliyan 200 ga mutanen da ‘yan ta’adda suka tarwatsa a jihar Kaduna. A yayin da ya neman samun takara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP. Haka a ranar Talatar da ta gabata ma ya ba da miliyan 300 ga wata qungiyar mata a jihar Legas.

Wannan kyaututtuka da gwamnan yake ta yi ba ji, ba gani, ya jawo masa shiga bakin Duniya. Har ma wasu suke ganin ya zama inuwar giginya, na nesa ka sha ta.

Domin kyautar ta zama ta ganin ido da neman suna, duk da jiharsa ta Ribas tana fama da matsalar rashin biyan albashin ma’aikata da haƙƙin masu ritaya. 

A wata tattaunawa da manema labarai, kakakin jam’iyyar APC, Darlington Nwauju, ya bayyana wannan taimako da gwamnan yake yi a matsayin almubazzaranci da rashin tunani a ɓangaren gwamnatin jihar Ribas.

Domin ba da waɗannan taimakon suna nuna rashin lissafin gwamnatin a daidai wannan lokaci da jiharsa ta ke cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.