Matatar man Ɗangote za ta fara samar da fetur ga Ƙasar Ghana

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ghana na jiran tsammanin fara aikin matatar man Dangote da za ta ragewa ƙasar matsalar wahalar makamashi.

Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur a Ƙasar Ghana, Mustapha Abdul-Hamid, ne ya bayyana hakan a kwanan nan.

A cewarsa, ƙasar Ghana za ta rage shigo da kayayyakin mai daga kasashen Turai da sauran ƙasashen ƙetare.

Shigo da kayayyakin man fetur daga ƙasashen waje na samar da nakasu da illa ga fannin makamashi a ƙasar Ghana saboda yadda ake tafiyar da harkokin mai a ƙasar. 

Ƙasar Ghana dai ta kasance daga jerin ƙasashen dake shigo da ɗanyen man fetur tun shekarar 2010, wannan ya sa take da rauni wajen tsayayyen farashin mai kasancewar shigo da shi ake daga Turai. 

Business Insider ta ruwaito cewa, shugaban hukumar kula da man fetur a ƙasar Ghana (NPA), Mustapaha Abdul-Hamid ya ce, fara aikin matatar Dangote zai kawo sauyi sosai a fannin fetur a Ghana. 

A cewarsa, ta hanyar samar da ganga 650,000 na man fetur, hakan zai kawo sauyi sosai tare da rage wahalar shigo da albarkatun man fetur zuwa ƙasar. 

Da ya ke magana a bikin bajekolin kasuwanci karo na 16 da aka yi a Legas, Abdul-Hamid ya ce, kammala aikin matatar man Ɗangote zai qara adadin samar da man fetur ga ƙasar Ghana da ma nahiyar Yammacin Afirka. 

Haka zalika, ya yaba wa gwamnatin Ghana a shirinta na kashe Dala miliyan 60 wajen gina turken man fetur a kan fili mai girman hekta 20,000 a yammacin ƙasar don ajiyar kayan mai. 

A cewarsa, aikin zai taimaka wajen haɓaka harkar mai, wanda ya haɗa da samar da albarkatu daban-daban na man fetur.