Ƙungiyar ‘yan jarida a Yobe ta raba gari da gwamnatin jihar

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu

Ƙungiyar ‘yan jarida (Yobe Correspondents’ Chapel) a jihar Yobe, ta bayyana ɗaukar matakin raba gari da Gwamnatin Jihar Yobe ta hanyar ƙaurace wa ɗaukar dukkan labaran aikace-aikacen gwamnatin jihar.

Ƙungiyar, a sanarwar bayan taron gaggawa wanda ta gudanar a ranar Jumma’a, 28 ga watan Oktoba, 2022 mai ɗauke da sa hannun Shugabanta da Sakatare; Ahmad I. Abba da Micheal Oshomah, sun bayyana ɗaukar matakin sakamakon cin zarafin da jami’an tsaron Gidan Gwamnati ke yi wa mambobinta.

Ƙungiyar ta ce ɗaukar matakin ya zo ne sakamakon tursasawa tare da cin zarafin da jami’an tsaron Gidan Gwamnati ke yi wa mambobinta da rashin kallon ƙimar da gwamnatin jihar ke nuna wa mambobinta.

A cewar sanarwar, “Saboda a matsayinmu na ɗaya daga cikin ginshiƙai huɗu a mulkin dimukuraɗiyya, ɓangaren da ke aikin sanar da al’umma dukkan abubuwan da ke faruwa a jihar Yobe.

“Babban abin takaici ne, a ce yau sama da shekara ɗaya amma babu fan jarida a jihar da ya yi fira kai tsaye da Gwamna Mai Mala Buni, sannan ƙungiyar ba ta taɓa samun wata gayyata a hukumance daga mai magana da yawun gwamnan, Alhaji Mamman Muhammed ba, kamar yadda aka saba yi a baya.

“Wannan ya haifar da mummunan gibi kuma ya yi tasiri ga ayyukan wakilan jaridun Nijeriya daban-daban waɗanda ke aiki a jihar Yobe.

“Wanda ya toshe wa dukkan ‘yan jaridu masu aikin yaɗa labaru samun duk wata damar kaiwa ga Gwamna Mai Mala Buni.

“Saboda irin yadda wannan abin takaici ke ci gaba da gudana a karkace, kuma duk da cewa tarihi ya nuna Gwamna ya taɓa riƙe shugaban kwamitin riƙo a jam’iyyar APC na ƙasa, inda ya shafe sama da shekaru 3 yana ganawa da manema labarai a Abuja da sauran sassan ƙasar nan, amma ya kasa ya tattauna da ‘yan jaridu a jiharsa.

“Duk da yadda al’ummar jihar suke kewar sanin manufofin gwamnatinsa, tsare-tsare tare da ayyukan da ya aiwatar a cikin waɗannan shekaru da ya yi a matsayin Gwamnan jihar.

“Wanda hakan ya jawo ƙungiyar ta yanke shawarar ilahirin mambobinta za su daina ɗaukar duk wani labari ko sanarwar manema labarai wanda gwamnatin jihar Yobe ta fitar har sai abin da hali ya yi.

“Haka kuma, mambobin ƙungiyar suna kira ga shugabannin hukumomin tsaro a Jihar Yobe da su wayar da kan jami’ansu su dena cin zarafin kafafen yaɗa labarai.”

“Ƙungiyar ta ga cewa ya zama dole ta ɗauki wannan muhimmin mataki a daidai wannan gaɓa, domin jawo hankalin dukkan masu ruwa-da-tsaki da hukumomin da suka dace, saboda su ɗauki ƙwaƙƙwaran matakin da ya dace tare da magance matsaloli da barazanar da manema labarai ke fuskanta a Yobe don gyara su cikin tsanaki.”

“A ƙarshe, muna sake nanata cewa ‘yan jarida masu aikin yaɗa labaru a Jihar Yobe suna sanar da jama’a tare da gwamnatin Jihar Yobe cewa, ba su ɗauki wannan matakin domin ra’ayin kansu ba, face don kasancewarsu a matsayin su na daga cikin ginshiƙan da ke taimakon ci gaba da ɗorewar mulkin dimokuraɗiyyar kasarmu Nijeriya.

“Har ila yau, yana da mahimmanci a lura cewa babban zaɓe mai zuwa yana da matuƙar muhimmanci a dimokuraɗiyyar ƙasarmu Nijeriya, don haka kuskure ne duk wani yunƙurin yi wa kafafen yaɗa labarai bi-ta-da-ƙulli,” inji sanarwar.