Ba Janar Ishaya ne daraktan yaƙin neman zaɓen Atiku a Kebbi ba – PDP

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kebbi ta musanta naɗa Janar Ishaya Bamaiyi (murabus) a matsayin daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jihar.

Kamar yadda shugaban Jam’iyyar PDP na jihar, Alhaji Usman Suru ya bayyana wa manema labarai a lokacin da yake zantawa a ranar Larabar da ta gabata a garin Birnin Kebbi, yayin da yake mayar da martani kan wani rahoto da aka samu ta yanar gizo da ya ayyana Janar Ishaya a matsayin daraktan yaƙin neman zaɓen ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa.

Ya bayyana cewa an jawo hankalin ‘ya’yan Jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi kan wata hira da manema labarai da Alhaji Kabiru Tanimu Turaki ya yi da kuma jaridar Blueprint Newspaper  ta Turanci ta wallafa a yanar gizo da ke cewa Jam’iyyar PDP ta naɗa Janar Ishaya ɗin daraktan yaƙin neman zaɓen Atiku na shugaban ƙasa a Kebbi.

“Tattaunawar da aka yi a kafafen yaɗa labarai da ake magana a kai da jama’a musamman ‘yan Jam’iyyar PDP na jihar Kebbi aka naɗa Janar Ishaya Bamaiyi a matsayin Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen shugaban qasa na jam’iyyar PDP a jihar Kebbi.

“Muna so mu bayyana dalla-dalla cewa naɗin shine tunanin Kabiru Tanimu Tukari ba na jam’iyya ba ne.

“Haqiqa an kafa tsarin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jihar Kebbi kamar yadda shugabannin jam’iyyar na ƙasa suka bayar da umurni wata ɗaya da ya gabata, maganar gaskiya ita ce majalisar yaƙin neman zaɓen Wazirin Adamawa ɗin tana ƙarƙashin jagorancin Dakta Bello Haliru,” inji shi.

Jam’iyyar PDP a Kebbi dai ana hasashen ta daɗe tana fama da masu yi mata angulu da kan zabo daga waɗansu da ke ikirarin su ne shugabannin ta da ke haɗa baki da gwamnatin Kebbi suna sayar da jam’iyya.