Gwamnan Kano ya kori Kwamishina kan kalaman tunzura al’umma

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sallami Kwamishinan Filaye da Safiyo na gwamnatin jihar, Adamu Aliyu Kibiya, daga muƙaminsa bayan zargin sa da furta kalaman tunzura al’umma.

Kazalika, sallamar ta shafi mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin wasanni da matasa, Yusuf Imam, wanda aka fi sani da Ogan Boye wanda shi ma ake zargi da furta kalaman da ba su dace ba a madadin gwamnatin.

Idan za a iya tunawa, a ƙarshen makon nan ne bidiyon jami’an gwamnatin suka rinƙa yawo a shafukan sada zumunta, inda suke furta kalamai game da shari’ar da ake yi kan zaɓen gwamnan jihar da ya gabata.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Baba Halilu Ɗantiye da kuma na shari’a, Haruna Isa Dederi suka karanta a daren ranar Juma’a, sun ce jami’an gwamnatin sun yi magana ba tare da izinin gwamna ba, sun kuma yi kalamai na tunzura al’umma sannan kuma sun ci zarafin Ƙataimakin Shugaban Ƙasa, Kashin Shettima.

A cikin kwanakin nan dai yanayin na siyasa ya ƙara zafafa gabanin hukuncin kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamna na jihar.

Inda manyan jam’iyyun jihar, NNPP da APC suka gudanar da addu’o’i da azumi domin neman nasara a shari’ar.

A baya dai ɗaya daga cikin alƙalan kotun ta yi zargin cewa akwai wasu da ke yunƙurin bai wa alƙalai da lauyoyin kotun cin hanci domin samun nasara a shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *