Guardiola zai ja ragamar wasan Man City da West Ham bayan dawowa daga jinya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ana sa ran Pep Guardiola zai koma Ingila ranar Laraba, domin jan ragamar wasan da Manchester City za ta kara da West Ham a gasar Firimiyar Ingila.

Ranar Asabar 16 ga watan Satumba City za ta ziyarci West Ham, domin fafatawa a wasan mako na biyar a babbar gasar tamaula ta Ingila.

City tana matakin farko a kan teburi da maki 12, bayan cin dukkan wasa huɗu da fara kakar nan, yayin da West Ham mai maki 10 take ta huɗu.

Guardiola, wanda ya yi jinya sakamakon ciwon baya, bai ja ragamar City wasan Firimiya da ta doke Sheffield United da Fulham a cikin watan Agusta ba.

Mataimakin Guardiola, Juanma Lillo ne ya ja ragamar wasan da City ta je ta ci Sheffield United 2-1 da wanda ta caskara Everton 5-1 a Etihad.

Daga ranar Laraba ‘yan wasa da dama za su fara komawa ƙungiyoyinsu, bayan da suka buga wa tawagoginsu tamaula.

Guardiola ya lashe Firimiya da FA Cup da Champions League a karon farko a City a bara.

Haka kuma ɗan ƙasar Sifaniya ya ɗauki UEFA Super Cup a dai kakar da ta wuce, bayan doke Sevilla 5-4 a bugun fenariti, bayan da suka tashi 1-1 a Athens.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *