Gwamnati ta amince da sabon ƙudirin dokar fallasa ɓarayin gwamnati

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta amince da sabuwar dokar kwarmato don fallasa ɓarayin gwamnati.

Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ce ta amince da dokar yayin zamanta na ranar Laraba.

A cewar Gwamnati, dokar za ta taimaka mata wajen ci gaba da yaƙi da rashawa a ƙasar nan.

Da take yi wa manema labarai ƙarin haske game da zaman Majalisar, Ministar Kuɗi, Zainab Ahmed ta ce: “Ma’aikatar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare ta gabatar da ƙudurori da dama a yau.”

Ta ce daga ciki har da dokar fallasa ɓarayin gwamnati ta 2022.

Ta ce dalilin wannan doka shi ne don ƙarfa yaƙi da rashawa da kuma ba da kariya ga masu fallasa ɓarayin gwamnati.