Kotu ta janye umarnin tsare Usman Baba

Daga BASHIR ISAH

Babbar Kotun Abuja ta janye umarnin da ta bayar kan tsare Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Usman Baba a gidan yari.

Hakan ya biyo bayan tabbacin da ya bayar ne kan cewa Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ƙarƙashin kulawarsa, za ta za zamo mai ɗa’a da biyayya ga dokoki da kare ’yancin ’yan ƙasa.

Kotun, ƙarƙashin Mai Shari’a Bolaji Olajuwon, ta janye umarnin nata a kan Baba ne yayin zaman da ta yi ranar Laraba.

Tuni Sufeto-Janar ɗin ya yaba wa kotun bisa janye umarninta a kansa.

Tun farko, Kotu ta ba da umarnin tsare Baba a kurkuku na wa’adin wata uku saboda rashin kiyaye umarnin Kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *