Gwamnati ta buƙaci bankuna su fara bayar da katin ɗan ƙasa haɗe da ATM

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta ba wa bankunan kasuwanci izinin fara ba wa abokan hulɗarsu katin cirar kuɗi na ATM da ke haɗe da katin shaidar ɗan ƙasa a wurin guda.

Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya sanar cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince bankuna su fara bayar da katin na bai-daya ba tare da sun caji kwastomomi ko sisi a kan kuɗin katin ATM da aka saba ba.

Ya ƙara da cewa“An ba wa bankuna izinin buga katunan Mastercard ko Visa da za su yi amfani a matsayin katin shaidar ɗan ƙasa ba tare da sun caji ’yan Nijeriya ƙarin kuɗi ba.

“Duk mai son karvar katin banki, sai ya sanar da su cewa mai haɗe da katin ɗan ƙasa yake so, sai su ba shi kati ɗaya da ya haɗe abubuwan biyu,” in ji Pantami.

Ya bayyana cewa, Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Kasa (NIMC) ta yi haka ne da haɗin gwiwar Babban Bankin Nijeriya (CBN) “domin sauƙaƙa wa duk mai buƙata samun katin ɗan ƙasa ta hannun bankinsa.”

Da yake jawabi bayan zaman ƙarshe na Majalisar Zartarwa ta Tarayya da gwamnatin Buhari ta gudanar, a Fadar Shugaban Ƙasa, Minista Pantami ya bayyana cewa Dokar NIMC ta 2007, ta wajabta wa ’yan Nijeriya mallakar lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN) ne kawai.

Ya ci gaba da cewa, “A lokacin mallakar katin shaidar ba dole ba ne, ra’ayi ne; Amma sai mutane suka riƙa kai wa NIMC ƙorafi cewa ba su samu katinsu na ɗan ƙasa ba.

“A kan haka ne a shekarar 2022 muka fito da katin shaidar ɗan ƙasa na zamani, wanda mutun zai iya saukewa a wayarsa, wanda kuma ke amfani ba lallai sai mutum ya buga shi a takarda ba.

“Duk da haka aka ci gaba da samun ƙorafi, musamman daga mazauna yankunan karkara, cewa suna buƙatar riƙe katinsu na ɗan aasa a hannu.

“Shi ya sa muka sauƙaƙa samun katin, inda NIMC da bankin CBN suka yi haɗin gwiwa domin tabbatar da ganin mutane za su iya zuwa bankunansu su karɓi katin ɗan ƙasa mai haɗe da ATM.”

Ministan ya shaida wa ’yan jarida cewa NIMC da CBN sun rattaba hannu kan alƙawarin tsare sirri da bayanan masu katunan shaidar

“Idan mutum ya nemi banki ya ba shi katin, kai-tsaye bankin zi tura wa NIMC, su kuma da zarar sun tantance suka tabbatar da sahihancin bayanan a rumbun adana bayanansu, sai su ba wa bankin izinin buga katin, nan take,” in ji shi.