Kirsimeti: Gwamnati ta sake ayyana ranakun hutu

Daga WAKILINMU

A karo na biyu, Gwamnatin Taraya ta sake sanar da ranakun hutun gama-gari albarkacin bukukuwan Kirsimeti da na Sabuwar Shekara.

Gwamnatin ta ayyana ranar 26 da 27 ga Disamban 2022, da kuma 2 ga Janairun 2023 a matsayin ranakun hutu don bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a madadin Gwamnati cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen taya Kiristoci ’yan Nijeriya da sauran ‘yan kasa murnar wadannan bukukuwa.

Haka nan, ya yi kira ga Kiristoci da su yi koyi da karantarwar Yesu Almasihu wajen yada kyawawan ɗabi’unsa a cikin al’umma.