Kirsimeti: FRSC ta tura jami’ai 1,769 da motocin sintiri 35 a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa FRSC, reshen Jihar Kaduna ta tura jami’ai aƙalla 1,769 da motoci 35 domin tabbatar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara ba tare da cikas ba a jihar.

Muƙaddashin kwamandan sashin, Garba Lawal ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kaduna.

Lawal ya ce ma’aikata 1,769 da aka tura sun haɗa da jami’ai 290, da Marshals 979 da kuma jami’a na musamman guda 500.

A cewarsa, an ɗauki matakin ne domin tabbatar da kiyaye doka a manyan titunan Kaduna, musamman a wannan bikin na Kirsimeti da yaqin neman zaɓe.

“Bugu da ƙari, baburan wutar lantarki guda biyar, motar kashe gobara ɗaya, motocin janye mota guda biyu, motocin ɗaukar marasa lafiya guda 10, biyu daga gwamnatin jihar Kaduna don bunqasa tallafin kayan aiki da jami’an tsaro, kayan aiki irinsu injinan cirewa, mazugi, kyamarorin jiki, bindiga da kuma jami’an sintiri.”

Ya yi bayanin cewa za a raba waɗannan ne ta hanyoyin da aka keɓe a matsayin wani ɓangare na matakan tabbatar da kiyaye haɗura tsakanin 20 ga Disamba zuwa 15 ga Janairu, 2023.

“An tsara su ne don magance hauhawar yawan zirga-zirgar ababen hawa da kuma keta dokokin zirga-zirgar ababen hawa, musamman a lokutan bukukuwa.

“Za mu yi yaƙi da masu yin tuƙin da ya wuce hankali, lodi fiye da kima, tafiye-tafiyen dare, rashin ingantacciyar tayar mota, rashin haƙuri, amfani da bel, amfani da waya, ɗora yara a gaban mota, da dai sauran abubuwan da doka ta hana.

“Saboda haka, za mu gudanar da aikin tura ma’aikata da kayan aiki masu yawa a kan manyan wuraren da ke da haɗari irin su Olam, Doka, Kakau da Jere a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja,” inji shi.

Ya ƙara da cewa atisayen zai kuma shaida yadda aka kafa sansanonin kula da ababen hawa da ceto, musamman a Rigachikun, Kwanan Farakwai da Dumbin Rauga da jami’an ‘yan sanda suka gudanar.

“Hanyoyin sun haxa da Kaduna-Abuja, Kaduna-Zaria, Zaria-Kano, Kaduna-Birnin Gwari da Kaduna-Kachia, dajin Kachia-Barde, titin Akwanga-Gwantu a matsayin wani ɓangare na matakan daƙile haɗarurrukan da suka shafi gudu a lokacin bukukuwan.

Muƙaddashin kwamandan ya tunatar da masu ababen hawa da sauran jama’a cewa jami’an su za su tsaurara sintiri a ƙarshen shekarar nan don “daƙile yin gudun da zai kai ga rasa rayukan jama’a.”

Ya buqaci jama’a masu tuƙa ababen hawa da su lura da kyau da ababen hawa a kan manyan hanyoyin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano musamman wuraren da suka hada da Olam Farm, Kakau, Katari, Jere, Audu Jangwam, Kwanan Tsintsiya, Lamban Zango.

Lawal ya gargaɗi masu ababen hawa da su tabbatar da bin ƙa’idojin zirga-zirgar ababen hawa tare da kula da ababen hawa a kai a kai, da yanayin lafiya da hankali, domin masu rai ne kaɗai ke iya yin biki.

“Rundunar tana yi wa masu ababen hawa fatan alheri da kuma yin sabuwar shekara mai albarka,” inji Lawal.