Nijeriya ta tafka asarar tiriliyan N64.3 a shekara huɗu – Bankin Duniya

Daga WAKILINMU

Bankin Duniya ya ce, Nijeriya ta tafka asarar kuɗi Dalar Amurka biliyan 144.1, kwatankwacin Naira tiriliyan 64.3.

Bankin ya ce rashin iya tattalin harkar canji daga bagaren Babban Bankin Najeriya (CBN) ne ya janyo wa ƙasar wannan asara daga 2017 zuwa 2021.

Ya ce yadda CBN ke tafiyar da harkokin canjinsa ya haifar da rarrabuwar ra’ayoyin masana tattalin arziki da masu sharhi kan lamurra.

Bayanan da Bankin Duniyar ya wallafa a shafinsa na intanet sun rashin iya tafiyar da sha’nin canjin daga ɓangaren CBN hakan ya sa kasar ta tafka asarar Dalar Amurka biliyan 144.1 daga 2017 daga 2021.