Wahalar fetur: Barazana ga bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara

*Duk da gargaɗin DSS ƙarancin fetur na gurgunta harkokin rayuwa
*’Yan Nijeriya sun koka da tsadar abinci da sufuri
*Mun samar da miliyoyin ayyuka a fannin noma – Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Daga dukkan alamu wahalar samun man fetur a Nijeriya cikin ’yan kwanakin nan yana matuƙar barazana ga samun walwala da jin daɗin al’ummar ƙasar a lokacin da suke ƙoƙarin gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara mai kamawa ta 2023.

A ranakun Lahadi da Litinin, 25 da 26 ga Disamba, 2022, za a gudanar da bikin ranar Kirsimeti, sannan kuma a ranar wata Lahadin ce za ta kasance 1 ga sabuwar shekara ta 2023. To, amma kawo yanzu an kwashe makonni da dama a na fama da ƙarancin man fetur a faɗin ƙasar, wanda da shi ne aka fi dogara wajen zirga-zirgar ababen hawa wajen tafiye-tafiyen mutane, sufurin kayan abinci da jigilar sauran kayayyakin amfani.

Duk da wa’adi da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta ba wa ’yan kasuwar man fetur, don kawo ƙarshen matsalar ƙarancin fetur da ake fama da shi a ƙasar, daga dukkan alamu lamarin ya ci tura, saboda ganin yadda matsalar ke ci gaba da taɓarɓarewa a wasu jihohi tana gurgunta harkokin zamantakewa da tattalin arziki.

Rahotanni sun bayyana cewa, gidajen mai kaɗan ne ke bayar da mai ga masu ababen hawa, shi ma kuma a farashi mai tsada ne.

A ranar 9 ga Disamba, 2022, ne Hukumar DSS ta bai wa kamfanoni da gidajen man fetur na ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki a harkar man fetur wa’adin sa’o’i 48, domin warware matsalar ƙarancin man fetur da ake fama da ita.

Hukumar DSS ta yi gargaɗin cewa, za ta bi diddigin kamfanonin da ke daƙile ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na samar da wadataccen man fetur ga ’yan Nijeriya.

A cewar rahoton da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) da ya zagaya da wasu gidajen man da ke Birnin Kebbi ya nuna cewa wasu gidajen mai da ke buɗe na sayar da mai a tsakanin Naira 280 zuwa 300 kan kowace lita.

Haka nan ya wakilan Blueprint Manhaja da suka ziyarci gidajen mai a jihohin Kano, Kaduna da Katsina ma duk kanwat ja ce.

Shugaban Ƙungiyar Ma’aikatan Sufurin Mota ta Ƙasa (NURTW) a babbat tashar motoci ta Kebbi (Sabuwar Tasha) dake Birnin Kebbi, Alhaji Garba Dan-Malam, ya ce, lamarin ya zama abin damuwa.

Dan-Malam, wanda ya bayyana fatansa na ganin gwamnati za ta shawo kan lamarin, ya ce ƙarancin da ake fama da shi na ɗan lokaci ya yi illa ga mambobinsa.

Ya lura cewa, ƙarancin man fetur da hauhawar farashinsa sun durƙusar da harkokin tattalin arziki na al’ummar Nijeriya, inda ya ce, idan har ana gudanar da harkokin kasuwanci, dole ne mutane da kayayyaki da ayyuka su tashi daga wannan wuri zuwa wani.

Shugaban ya ce, duk da ƙarin farashin man fetur, farashin sufurin da ’yan ƙungiyar ke karva yana da sauƙi.

Sai dai ya koka da yadda ’yan ƙungiyar ba su ji daɗin halin da ake ciki a yanzu ba.

Da aka tuntuɓi shugaban ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Nijeriya, IPMAN, shiyyar Arewa maso Yamma, Alhaji Muhammad Tila, ya zargi hukumar kula da albarkatun man fetur ta ƙasa (NNPC) kan matsalar da ta daɗe tana fama da ita.

Ya ce, kamfanin na NNPC ne kaɗai ke da alhakin shigo da man fetur a ƙasar nan, inda ya ce direbobi da dama sun shafe kwanaki bakwai zuwa takwas suna yin layukan ɗauke kaya zuwa Arewa.

Shugaban hukumar ya tuna cewa, Hukuma DSS ta baiwa masu ruwa da tsaki a harkar man fetur wa’adin sa’o’i 48, amma duk da haka, ba a samu man ba, musamman a Arewa.

Tila ya ce, a da a baya Nijeriya tana da jiragen ruwa 10 zuwa 20 a cikin teku suna jira su tashi, amma yanzu da ƙyar ka ga jiragen biyu a gaɓar tekun Nijeriya.

Ya jaddada buƙatar gwamnati ta ba da dama ga ma’ajiyar ajiya masu zaman kansu su shigo da kayayyakin.

A halin da ake ciki, Ƙungiyar Dillalan Man Fetur Mai Zaman Kanta (IPMAN), reshen Aba Depot, ta ce, yawan shigo da mai shi ne kaɗai mafita ga matsalar man da ke addabar ƙasar.

Shugaban hukumar, Mazi Oliver Okolo, wanda ya bayyana haka bayan wata ganawa da kwamishinan man fetur na Jihar Abiya, Cif Sam Nwangang a ƙarshen mako, ya amince cewa man da ake da shi bai wadatar da ’yan Nijeriya ba.

Barazana ga bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekarar:

’Yan Nijeriya sun nuna matuƙar ɓacin rai kan tsadar abinci da safuri gabanin bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Fiye da kashi 80 cikin 100 na waɗanda suka zanta da Blueprint Manhaja sun ce, a bana, ya zama mafi muni, musamman yadda farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi a garuruwa daban-daban na ƙasar.

Wata ’yar kasuwa mai suna Hope Okolie a Legas ta ce, farashin shinkafa da man gyada da tumatur ne suka fi tashi.

“Idan ka cire waɗannan abubuwan daga Kirsimeti, me kuma kake da shi,” inji ta.

Victoria Oluemo, wata ma’aikaciyar banki ta ce, abinci kawai mutane me magana a kai, domin kuwa idan ka koma kan tufafi sai dai ka rufe baki. A cewarta, kwanakin sayen kayan sawa sun kusa shuɗewa ganin irin yadda tufafi ya yi tsadar gaske.

“Abin da kuke gani yawancin mutane suna saya yanzu, kayan sawa ne na gwanjo. Wani abu da mutane suka saba ɓoyewa don saya a shekarun baya, yanzu ya ɗaukaka.

“A gaskiya ma, yawancin wuraren sayar da sababbin kaya da kuke tsammani suna sayar da kayan gwajon, domin mutane ba sa iya sayen kayan kanti,” ta koka.

Wata mai sayar da kayan abinci a Legas Onyeshile Shola ta shaidawa Blueprint cewa, buhun shinkafa a yanzu ana sayar da shi tsakanin Naira 45,000 zuwa sama da 50,000, ya danganta da darajar shinkafar.

“Za ku yi mamakin sanin cewa, shinkafar da ake nomawa a cikin gida ta fi tsada,” inji ta.
Olu Samson, wani manazarci a Legas, ya danganta wannan mummunar yanayi da ta shafi yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine.

A cewarsa, duk da cewa yaƙin ya yi nisa sosai da Nijeriya, amma saboda toshewar ruwan ƙasa da ƙasa, an daƙile safarar kayayyaki sosai.

“Kada a yaudare mu, yawancin abincin da muke ci a ƙasar nan daga wasu ƙasashem waje su ke zuwa. Hatta waɗanda ya kamata mu noma a nan Nijeriya, sun gagara saboda rashin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.

Haka kuma gwamnati ta hana a shigo da wasu kayayyaki cikin ƙasar nan, inda ta tabbatar da cewa ana shigo da su ne a kan farashi mai tsada ga masu amfani da su, wanda dole su ci ko kuma su gamu da ajalinsu.”

Olu ya ci gaba da nazarinsa inda ya ce, halin da ake ciki, yaƙin Rasha da Ukraine ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki a mafi yawan ƙasashen duniya, kuma sakamakon abin da kuke gani a kasuwannin Nijeriya shi ne abin da ake nufi da hauhawar farashin kayayyaki daga ƙasashen waje.

Victor Ojo, wani mai jigilar kayayyaki ya ce, ƙaruwar yanayin sufurin ya samo asali ne saboda dogayen layukan da ake yi a gidan mai, wanda a mafi yawan lokuta ba sa sayar da komai.

Ya yi imanin cewa, idan yanayin ya inganta, farashin sufuri na iya saukowa a wannan makon.

Mun samar da ayyuka miliyan 13 – Buhari

To, sai dai kuma, a ƙoƙarinsa na nuna irin rawar da gwamnatinsa ke yi wajen rage raɗaɗin talauci da ƙuncin rayuwa da ’yan ƙasar tasa ke fama da su, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bugu ƙirji, inda ya gaya wa ƙasashen duniya cewa, a wa’adin mulkinsa Gwamnatin Tarayya ta samar da ayyukan yi kai tsaye ga mutune sama da miliyan 13 a cikin shekaru bakwai da rabi da suka gabata.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wani zama na mu’amala da Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka (USIP), Cibiyar ’yan Jamhuriyya ta ƙasa da ƙasa da kuma gidauniyar ƙasa da ƙasa.

A wata sanarwa a ranar Asabar, 17 ga watan Disamba, 2022, mai magana da yawun shugaban ƙasa, Garba Shehu, ya ruwaito Buhari yana faɗin cewa kutsa kai cikin harkar noma, wanda babban bankin Nijeriya (CBN) ke jagoranta ya canja ƙasar daga mai shigo da shinkafa zuwa mai noman shinkafa don dogaro da kai.

Buhari ya kuma ce, mayar da hankali kan fannin noma ya sanya Nijeriya cikin yanayi mai kyau don shawo kan matsaloli kamar annobar Korona da yaƙin Rasha da Ukraine kan samar da abinci a duniya.

Ya ce, juyin-juya halin da ake samu a fannin ya inganta iyawa da ingancin ƙasar wajen ƙarawa da inganta noma da asarar bayan girbi.

“Ɓangaren da ba na man fetur ba shi ne makomar tattalin arzikinmu kuma ina fatan gwamnatocin gaba za su ƙarfafa kan nasarorin da muka samu a ƙarƙashin jagorancina,” inji shi.

Ya ce, “Za ku yarda da ni cewa yaqin Rasha da Ukraine ya tilasta wa ƙasashe da dama yin gyare-gyare da kuma gyara manufofin da za su tinkari ƙalubalen da rikicin ke haifarwa.”

Shugaba Buhari ya kuma shawarci ƙasashen yammacin duniya da kada su yi gaggawar dogaro da amfani da man fetur domin samun ingantacciyar yanayi.