Taƙaita cire tsabar kuɗi da sauran batutuwa

Manufar cire kuɗaɗe da Babban Bankin Nijeriya CBN ya yi a baya-bayan nan, wanda zai taqaita adadin kaɗaɗen da mutane da kamfanoni za su iya fitarwa a kowane mako, ya sha suka daga ’yan siyasa da sauran ’yan Nijeriya. Sabuwar manufar ta sanya mafi girman cire kuɗi a kowane mako akan Naira 100,000 ga kowane mutum da 500,000 ga ƙungiyoyi da kamfanoni. Manufar cire tsabar kuɗin ta zo ne bayan da CBN ya sake fasalin takardar Naira 200, 500, da 1000.

Manufar babban bankin zai duba yawan kuɗaɗen da ake samu a wajen tsarin banki. A cewar CBN, kusan kashi 85 cikin 100 na kuɗaɗen da ake zagayawa a waje suna wajen bankunan ne, kuma hakan ya gurgunta tattalin arzikin ƙasar wajen aikata laifuka daban-daban, ciki har da tara kuɗaɗen. Ana kallon taqaita fitar da tsabar kuɗi a matsayin wani mataki da hukumar kuɗi ta ɗauka wajen daqile sayen quri’u da ’yan siyasa ke yi gabanin babban zaven 2023, da kuma duba hauhawar farashin kayayyaki, da dai sauransu. Sabbin hauhawar farashin kayayyaki na watan Disamba shine kashi 21.4 bisa 100.

Duk da fa’idar da aka yi hasashen za a samu na sabuwar manufar cire kuɗi ta CBN a ƙarƙashin Godwin Emefiele, ‘yan Nijeriya da dama na adawa da shi kuma waɗanda ke goyon bayan manufar suna cikin ‘yan tsiraru. ’Yan siyasar Nijeriya da dama sun nuna adawa da shirin. Wataƙila hakan na iya yin bayanin dalilin da ya sa Majalisar Dattawa ta yi kira da a sake duba lamarin taƙaita cire tsabar kuɗi ga ƙungiyoyin jama’a da na kasuwanci. ’Yan majalisar dai sun yi hasashen cewa matakin rage yawan kuɗaɗen da aka yi a yanzu zai gurgunta yaƙin neman zaɓe da sauran dabaru na babban zaɓe mai zuwa.

Don haka, majalisar dattawa ta umarci kwamitinta mai kula da harkokin bankuna, inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi, da ya fara sa ido a kan babban bankin CBN, kan ƙudirinsa na yin gyara a kan ƙa’idojin cire kuɗi da kuma kai rahoton sakamakon ga majalisar. Sai dai majalisar dattijai ta goyi bayan aiwatar da tsarin biyan kuɗin canji da babban bankin CBN ya ɓullo da shi, muddin babban bankin ya yi nazari kan wasu tanade-tanade na manufofin rage yawan kuɗi daidai da abubuwan da ake ciki a yanzu.

Sai dai wasu daga cikin ’yan majalisar wakilai sun bayyana matakin cire kuɗaɗen a matsayin abin da bai dace ba, don haka suka buƙaci a dakatar da shi. Yawancinsu sun yi kira ga Gwamnan CBN ya bayyana a gaban zauren majalisar a ranar 20 ga watan Disamba. Masu adawa da wannan manufa sun ce bai yi la’akari da buƙatun yau da kullun ba, ciki har da mazauna karkara. Sun kuma nuna cewa CBN bai yi cikakken tuntuɓa ba kafin ya ɗauki matakin.

Sai dai Gwamnan Babban Bankin na CBN ya yi nuni da cewa, za a iya sake duba iyakar janyewar zuwa sama, amma bai fayyace ko nawa ba. Yayin da yake yanke hukuncin dakatar da manufar, Emefiele ya dage cewa matakin yana da fa’ida ga tattalin arzikin qasa baki ɗaya. Har ila yau, wata babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis ta qi amincewa da umarnin ƙungiyar da ke neman hana CBN da gwamnatin tarayya cigaba da wa’adin ranar 31 ga watan Junairu, 2023, inda za a daina amfani da tsafaffin takardun kuɗi na yanzu. Hukuncin kotun ya zo ne a ranar da wasu masu zanga-zangar qarqashin ƙungiyar ‘Initiatives for Patriotic Nigerians’ da wasu ƙungiyoyin farar hula (CSO) suka yi wa harabar majalisar dokokin ƙasar ƙawanya domin nuna goyon bayansu ga manufar CBN.

Ƙungiyar dai ta dage cewa a bar manufar ta cigaba da tafiyar da harkokinta, domin hakan zai taimaka wajen daidaita farashin canji da kuma samar da sahihin zaɓe mai inganci a shekara mai zuwa. Mun yi imanin cewa manufar taqaita cire kuɗi za ta taimaka wajen bincika laifuka da satar kuɗi idan an aiwatar da su ba tare da wata matsala ba. Yayin da lokaci ya bada dama, CBN na iya gyara kura-kuran da aka samu. Daidaita ƙa’idar taƙaita cire kuɗi wani abu ne da ya kamata hukumar hada-hadar kuɗi ta gaggauta yi, kamar yadda majalisar dattawa da sauran ’yan Nijeriya suka ba da shawara.

Sai dai dole ne CBN ya tabbatar da cewa hakan bai ƙara tsadar kasuwanci a ƙasar nan ba. Manufar taƙaita cire tsabar kuɗi ita kaɗai ba za ta iya magance matsalar tattalin arzikin ba. Gaskiya ita ce, tattalin arzikinmu yana cikin mawuyacin hali kuma yana buƙatar kyawawan manufofi don sake fasalin abubuwa. Saboda haka, a halin yanzu kula da tattalin arziki ya fi komai amfani.