Shin ya kamata a kama gwamnan CBN?

Assalam alaikum. Ina godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki. Allah Ya cigaba da taimakon jaridar Blurprint.

A Nijeriya dai akan yi wasu abubuwa masu kama da wasan kwaikwayo. Rahotannin da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai na cewa Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS na shirin kama gwamnan babban bankin Nijeriya CBN, Godwin Emefiele.

Wata babbar kotu a Abuja babban birnin ƙasar ta yi watsi da buƙatar DSS ta kamawa da tsare Emefiele.

DSS na tuhumar Godwin da laifukan da suka shafi taimakawa ta’addanci, sai dai kotun ta ce hukumar ta koma ta samo ƙwararan hujjoji da shaidu kafin ta sake dawowa gabanta kan batun.

Abin da kotu ta ce game da batun Emefiele
Wani mai suna US Gambarawa shi ne ya shigar da ƙarar a madadin hukumar tsaron farin kaya ta DSS a ranar 7 ga watan Disambar 2022.

Tuhumar mai lamba FHC /ABJ/CS/2255/2022, ta nuna shari’ar tsakanin DSS da gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele.

DSS na zargin Godwin Emefiele, da tallafawa ta’addanci da kuɗaɗe hakan ya saɓa wa doka ya kuma aikata laifi kan tattalin arziki.

Mai shari’a John Terhemba Tsoho da aka gabatar da ƙarar gaban shi ya yi watsi da ita.

Ya ce, DSS ba ta gabatar da wata kwakkwarar shaidar da ta nuna gwamnan CBN ɗin ya aikata laifin ba, sannan kamata ya yi ace shugaba Muhammadu Buhari ya san da batun.

Takardun tuhumar da kotun ta yi watsi da su, da sashen BBC Pigin ya gani, ya nuna alƙalin babbar kotun ne ya ɗauki matakin.

A hukuncin da ya zartar, Alƙalin ya yi bayani kan wasu bayanai da aka yi su a dunƙule da ya buƙaci a warware da yin bayani dalla-dalla, inda aka ambaci Godwin Emefiele ba tare da an faɗi muƙaminsa na Gwamnan babban bankin Nijeriya ba.

Alqali Tsoho ya qara da cewa, “DSS ba su yi gamsasshen bayani kan ko wanda suke ƙara mai suna Godwin Emefiele gwamnann CBN ne ko kuma wani mutum mai irin sunansa na daban, don haka ana buƙatar wannan bayani.

“Mutane za su yi mamaki da rudani ko wanda ake tuhumar Emefiele na CBN ne ko a’a, saboda ana magana ne fa a kan ɗaya daga cikin babban jami’in gwamnatin tarayya.”

Mai Shari’a Tsoho, ya kuma kafe cewa kamata ya yi tuhumar da DSS suka gabatar ta samu rattaba hannun shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari tun da shi ne ya naɗa Emefiele muƙamin.

“Lamarin ya yi kama da kotun na son fakewa da guzuma ne ta harɓi karsana, ta hanyar amfani da kotun wajen lulluɓe abin da suka aikata ba daidai ba da sun san ya saɓa wa doka kuma ba za a amince da shi ba.

“Wannan dalilin ne ya sanya ba mu amince da ƙarar da suka shigar ba, har sai sun gabatar da kwakkwarar hujja sannan za mu saurare su, amma ayanzu kam mun yi watsi da batun,” inji Alƙali Tsoho.

Ana ikirarin amtsalar da Emefiele ke ciki na da alaƙa da sauya takardun Naira.

Tun lokacin da Babban Bankin Nijeriya CBN ya sanar da sabunta wasu daga cikin takardun naira, aka fara matsawa Godwin Emefiele lamba.

Majalisar dattijan Nijeriya ta nuna rashin amincewa da wasu daga cikin tsare-tsaren sabbin kuɗin, hakan ya biyo bayan bayanan Ministar kuɗin Nijeriya Zainab Ahmad da ta ce sam ba ta da masaniya kan batun.

Har wa yau, majalisar wakilai ma ta gayyaci gwamnan CBN domin amsa tambayoyi kan sabbin kuɗaɗen da kuma yadda zai shafi tattalin arzikin Nijeriya.

A ranar Litinin wasu daga cikin lauyoyin ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam, da jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin farar hula sun fantsama tituna zanga-zanga.

Masu boren ƙarƙashin gamayyar ƙungiyoyin farar hula, sun ce DSS ta maka Emiefele gaban kotu ne domin su bata masa suna.
Sun yi kiran Shugaba Muhammadu Buhari da Ministan Shari’a Abubakar Malami su shiga batun.

DSS ta ce batun kare tsaron ƙasa ake yi
DSS ta yi ƙarin bayanin cewa tana bincike ne kan duk wani abu da ya shafi tsaron ƙasa. Kuma ayyukan da suke yi ya shafi ‘yan Nijeriya ne baki ɗaya.

Mai magana da yawun hukumar DSS, Peter Afunanya, ya fitar da sanarwa a ciki yana cewa wasu mutane na yaɗa farfaganda domin ɓata musu suna da aiki.

“Za mu ci gaba da aiki da bayyana sakamakon bincike ga ‘yan ƙasa ba tare da ƙumbiya-ƙumbiya ba, za mu sanar da waɗanda lamarin ya shafa ba tare da ɓoye-ɓoye ba,” inji sanarwar.

“Babu wata farfaganda da za ta yi tasiri a kanmu, ko wani abu da zai tsorata ni damu ba, ba bu wata barazana da za ta yi tasiri a kanmu.”

Allah Ya sa mu dace.

Wasiƙa daga MUSTAPHA MUSA, 08168716583.