Hajjin 2021: Legas za ta soma yi wa maniyyata bitar mako-mako

Daga WAKILINMU

A matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen hajjin bana, Gwamnatin Jihar Legas ta ce za ta soma gudanar da taron bita na mako-mako ga maniyyatan jihar domin faɗakar da su game da harkokin hajji.

Bayanan Hukumar Kula da Walwalar Maniyyata ta Jihar sun nuna cewa, Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Jihar Legas, Prince Anofiu Olanrewaju Elegushi, shi ne zai jagoranci ƙaddamar da shirin bitar nan ba da daɗewa ba.

A sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, Sakataren hukumar, Mr. Rahman Ishola, ya ce an shirya gudanar da tarurrukan ne domin bada horo ga sabbin maniyyatan jihar da ma waɗanda ke niyar sake komawa kan abubuwan da aikin hajji ya ƙunsa.

Ya ƙara da cewa shirin zai kankama ne daga ranar Asabar, 22 ga Mayu, 2021 a tsakanin ƙananan hukumomi 18 na jihar. Tare da cewa nufin shirin ne ƙarfafa ilimin maniyyatan kan sha’anin hajji da kuma kimtsa su yadda ya kamata wajen sanin ƙa’idojin hajjin bana da aka tsara.

Haka nan ya bada tabbacin an tanadi ƙwararrun malamai da za su yi jawabi yayin tarurrukan, kana ya jaddada aniyar gwamnatin jihar wajen tabbatar da cewa ba a samu wani akasi ba yayin gudanar da hajjin na bana.

Daga nan, Ishola ya shawarci ɗaukacin maniyyatan da su ɗauki shirin da muhimmanci domin samun zarafin tatsar ilimi daga jerin malaman da za su faɗakar da su da kuma taimaka wa gwamnatin jihar wajen cim ma manufarta kan shirin.

A ƙarshe, sakataren hukumar ya roƙi malaman da za su yi fama da jawabai da su maida hankulansu kan batutuwan da aka tsara gabatarwa a wajen tarurrukan. Kana su bada haɗin kansu ga jami’an gwamnati da aka wakilta don su sanya ido kan yadda shirin zai gudana.

Haka nan, ya gargaɗe su a kan su guji karɓar na-goro a hannun maniyyata saboda a cewarsa, duk malamin ko jami’in da aka kama da laifin aikata hakan za a hukunta shi daidai da doka.