Har yanzu ana kulle a aure?

Tare Da AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da sake haɗuwa a filin Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wannan mako kuma, mun kawo muku bayani a kan yadda wasu mazan aure musamman ma mazajen Hausawa waɗanda suke yi wa iyalansu kulle.

Menene kulle?

Kulle shi ne a hana mace ta fita ko ta yi mu’amala da waɗanda take so. Yawancin mazan Hausawa suna da kulle amma sai dai yayin da wasu mazan suke da sauƙi wajen mu’amala da tafiyar da iyali, wasu mazan kuma suna da zafin kishi da tsaurarawa. A yau za mu yi magana a kan masu tsaurarawar ne.

Kodayake, musulunci ya koyar da mu yadda za mu yi zaman aure. Sannan ya zana wa kowa haƙƙoƙinsa a cikin zamantakewar aure. Inda aka nuna cewa, namiji shi ne shugaba kuma mai tsayawa ne a kan mata. Amma kuma ko ya halatta yadda wasu mazan suke tsaurarawa a wajen kulle?

Bayan an yi aure miji yana gani matar nan ta zama mallakinsa. Don haka, zai yi duk wasu abubuwa da zai wa kansa garkuwa don ta cigaba da zama mallakinsa shi kaɗai.

Kuma ta dinga masa biyayya tana jin maganarsa shi ɗaya. Sai ya fara bin wasu hanyoyi da za su taimaka masa.

Hanyoyin da wasu mazan suke bi don yi wa mata kulle:

Na farko maza suna hana matarsu fita ko da zuwa nan da can. Sai gidan wanda suka yi niyya. Wani gidan iyayenta ma sai ta yi shekara da shekaru ba ta leƙa ba.

Saboda yana gudun kada ta dinga haɗuwa da wasu mutanen ko da kuwa yanuwanta ne, domin kada su hure mata kunne a kansa. Saboda yana ganin rashin wayonta ko ƙarancin shekarunta.

Sannan wani kuma yana tunanin idan tana haɗuwa da wasu ko da ‘yanuwanta ne da mazajensu suka fi shi samu za ta raina ƙoƙarinsa.

Wani kuma matarsa ce kawai ba ya son kowa ya gani. Wani idan ba danginsa ne suke sabga ba, ba zai bar ta ta je ba. Ko sabga ake a danginta ita kuma, ba ta da tabbas ko zai bar ta ta je. Wani ko asibiti da ya zama lalura ba ya son matarsa ta je.

Irin waɗannan mazaje sukan yi ƙoƙarin raba mace da kowa. Ta yadda za ta ƙara dogara da shi, ta dinga tsoron rabuwa da shi saboda ta rabu da kowa sanadiyyarsa. Ta zam ba ta da kowa, sai shi.

Na biyu, wasu mazan sukan hana kowa ya kawo wa matarsu ziyara sai wanda suka ga dama, suka yi niyya. Wani ko da ƙannenta maza ma sai ya hana su zuwa gidanta saboda wai kada su kalle masa matarsa.

Abu na uku da namiji mai kulle yake yi shi ne, ƙwace wayarta don kada ta yi mu’amala da kowa. Wani mai sauƙi-sauƙi ne ma zai qwace layukan da mutane suka santa da shi ya ba ta sabon layi. Saboda ya yanke mata mu’amala da mutanenta na da kafin ta shigo gidansa.

Wani kuma sai ya ƙwace babbar wayarta ya bar mata ƙarama wacce ba za ta iya hawa yanar gizo da ita ba.

Saboda yana tsoro kada tarbiyyarta ta gurvace. Wani kuma zai bar ta da wayar amma kullum cikin sa ido yake da bincike a wayar saboda kada ta yi mu’amala da waɗanda ba ya buƙata.

Na huɗu kuma shi ne, maza masu kulle sukan hana mata sana’a ko aiki ko cigaba da karatu. Yana ganin ƙarin karatun zai sa idonta ya ƙara buɗewa ta raina shi.

Wani kuma yana ganin yin sana’a da aiki zai sa ta tara dukiya ta kasa yi masa biyayya saboda ba abinda take nema a wajensa.

Idan kuwa ya hana ta neman na kanta, ai dole ta zo masa da ‘yar murya ya ba ta wani abu. Shi kuma sannan zai nuna mulki.

Na biyar kuma, hana ta yin shigar da ranta yake so ko da a cikin gida ne. Akwai mazan da sam mace ko biki za ta je ba za ta yi shigar da take so ba ta yi ado.

Sai ya umarce ta ta sa doguwar riga da zumbulelen hijabi a kai. Kuma duk zafi haka za ta fita. Wani ko cikin gidanta ba ta isa ta yi shiga irin wacce mata suke yi don faranta wa miji rai ba. Hasali shi shigar ma takaici take sanya masa.

Ko yaransa waɗanda ba nata ba ne idan maza ne ba ya so su kalle ta. Sai kishi ya kama shi. Wani ma fa yaran ƙanane, ba su san wata sha’awa ba. Amma kishi yake da su.

A nan za mu tsaya, sai mako na gaba idan Allah ya kai mu, za mu ci gaba.